Abbas Abubakar ya bayyana abin da yasa ya kashe matar kawunsa

Abbas Abubakar ya bayyana abin da yasa ya kashe matar kawunsa

Wani matashi dan shekara 20, Abbas Abubakar mazaunin kauyen Kissayip cikin karamar hukumar Bassa ta jahar Filato ya bayyana ma duniya dalilin da yasa ya kashe matar kawunsa, kanin mahaifinsa inji rahoton jaridar Daily Trust.

Abba ya bayyana cewa ya kashe matar ne sakamakon zarginta da yake yi da kashe wani gudan kawunsa, sa’annan ya kara da cewa ita ce wanda ta kashe masa shanunsa.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Buhari ya rattafa hannu kan dokar haramta ba-haya a bainar jama’a

Abbas ya bayyana haka ne yayin da Yansanda suka gabatar dasu a gaban manema labaru a babban ofishin Yansandan jahar Filato a ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, inda yace matar ta tabbatar da kisan kawun nasa ta hanyar cika baki da nuna isa, sa’annan ta yi barazanar kashe shi shima, da danginsu duka.

“A gaskiya dai bana cikin hayyacina a lokacin dana aikata wanann laifi, ji na yi kamar asiri aka yi min, amma bayan na aikata laifin sai kuma na fahimci girman abin da na aikata, a yanzu na yi dana sanin laifin dana aikata.” Inji shi.

Da yake bayanin yadda kanin mahafin nasa ya rasu, Abbas yace: “Ba shi da lafiya ne, a lokacin da muke kan hanyar kai shi wurin wani mai maganin gargajiya, sai ya fara kiran sunanta yana zarginta da yi masa asiri, ita da kanta ma tabbatar min cewa ita ta kashe shi.”

A nasa jawabin, kwamishinan Yansandan jahar, Isaac Akinmoyede ya bayyana cewa a ranar 13 ga watan Nuwamba ne wani mutumi mai suna Maitala Bako ya kawo mana rahoto daga kauyen Kissayip cewa wani dan bindiga ya kashe masa mata, mai suna Fatima Maitala.

Sai dai kwamishinan yace Maitala ya bayyana musu yana zargin Abbas Abubakar, Haruna Umar da Hadiza Abdullahi da kisan matar tasa, musamman saboda makiyan Fatima ne.

Daga nan sai Yansanda suka kamasu, kuma a yayin da yake amsa tambayoyi ne Abbas ya amsa laifinsa, har ma ya jagoranci Yansanda zuwa inda ya boye bindigar tasa inda muka gano wata bindiga mai baki daya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel