Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

Bidiyon wani almajiri yana Sallah a kan dakalin coci ya dauki hankulan mutane

- Bidiyon wani yaro musulmi ya karade kafafen sada zumunta

- An ga karamin yaron ne yana Sallah a gaban wata majami’a

- Bidiyon ya kawo cece-kuce, inda mutane da yawa ke tofa albarkacin bakinsu

Addini abu ne da yakamata a ce ya hada kan mutane. Amma a Najeriya kuwa, ya zama babban abunda ke kawo cece-kuce. Kowanne bangare na kokarin nuna yafi dayan bangare ko a wajen ubangiji.

A Najeriya, muna da addinnai manya guda biyu ne, musulunci da addinin kirista. Suna zaman lafiya amma wasu lokuta, a kan samu rashin jituwa a tsakaninsu.

Hoton wani wani karamin yaro yana Sallah a kusa da coci ya janyo cece-kuce
Hoton wani wani karamin yaro yana Sallah kusa da coci
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Dakarun NAF sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa

A cikin kwanakin nan ne, wani bidiyo ya dinga tashe a kafafen sada zumuntar zamani. Bidiyon na nuna wani karamin yaro ne, yana Sallah a gaban wata majami’a.

Wani wanda bai iya gani ya kyale ne ya nadi bidiyon; abinda ya jawo maganganu kala-kala a kafafen sada zumuntar zamani.

Sananniyar mai rajin kare hakkin dan adam, Aisha Yesufu ta ce, “Idan yaron nan ya samu dama, zai ajiye kwanon bararsa ne kuma ya shige majami’ar nan. Iyayensa da suka watsar dashi a titi zasu fara cewa, an sace mana danmu kuma an mayar da shi kirista. Gungun munafukai!”

Ga tsokacin da John Ade yayi: “Addinin kirista na koyarda hakuri da mutane, kuma yaron Sallah yake ba ihu ba ko wani abu daban da zai kawo hayaniya ba. Darasin da yake nunawa a nan, shine hakuri da mutane.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel