Saurayi a Kano ya halaka babban mutum saboda ya haska fuskar budurwarsa da Mota

Saurayi a Kano ya halaka babban mutum saboda ya haska fuskar budurwarsa da Mota

Wani saurayi dan shekara 22, Ibrahim Magaji dake kauyen Kosawa cikin karamar hukumar Kura ta jahar Kano ya jefa kansa cikin halin tsaka mai wuya bayan ya kashe wani mutumi daya haska fuskar budurwarsa da fitilar Mota.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Magaji ya aikata wannan danyen aiki ne a kauyen Dakasoye dake cikin karamar hukumar Garun Malam, inda ya je tadi wajen budurwarsa a ranar Lahadin da ta gabata.

KU KARANTA: Halima Dangote da manyan daraktoci 5 sun ajiye aiki daga kamfanin Dangote

Suna tsaye da budurwarsa suna hira ne kwatsam sai wani bawan Allah mai suna Auwalu Hussaini ya danno hasken filitar motarsa, inda a cewarsa Magaji hasken bai tsaya ko ina ba sai a fuskar sahibarsa, hakan kuma ya harzukashi ya tari Auwalu da rikici.

A cewar kaakakin Yansandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, tabbas hakan ya faru, kuma nan take Magaji yah au Auwal da duka har sai daya fiddashi daga cikin hayyacinsa, da kyar aka garzaya da Auwallu babban asibitin Kura, inda a can aka tabbatar da mutuwarsa, amma tuni gogan naku ya cika wandonsa da iska.

Daga bisani bisa umarnin kwamishinan Yansandan jahar Kano, Ahmed Iliyasu ne jami’an Yansanda na rundunar Puff-Adder suka kamo Magaji da misalin karfe 10 na daren Lahadin da abin ya faru.

“Kwamishinan Yansanda ya umarci a mika batun zuwa sashin binciken kwakwaf domin gudanar da binciken sirri a kan lamarin, amma binciken farko farko ya tabbatar da cewa wanda ake zargi ya kashe mutumin ne saboda ya haska fuskar budurwarsa da fitilar motarsa.” Inji shi.

A wani labarin kuma, jami’ar gwamnatin tarayya dake garin Fatakwal na jahar Ribas ta kaddamar da sabuwar dokar yaki da cin zarafin dalibai mata, inda tace daga yau ta haramta duk wata alaka data shafi rungumar juna tsakanin Malamai da dalibai Mata.

Shugaban jami’ar, Farfesa Ndowa E.S ne ya bayyana haka a wani taron kaddamar da sabuwar dokar, inda yace sun samar da wannan doka ne domin tabbatar da kare malamai da dalibai daga cin zarafi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel