Tab dijan! Za'a tura yan sanda 35,200 Kogi, 31,041 Bayelsa rana zabe

Tab dijan! Za'a tura yan sanda 35,200 Kogi, 31,041 Bayelsa rana zabe

Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, IGP Mohammed Adamu, ya ce hukumar za ta tura jami'an yan sanda 66,341 domin tsaron ranar 16 ga Nuwamba da za'a gudanar da zaben gwamnan jihar Kogi da Bayelsa.

Adamu ya bayyana hakan ne ranar Juma'a a Abuja wajen taron kwamitin tabbatar da tsaron zabe da shugaban hukumar INEC, Mahmood Yakubu, ya shirya.

A cewarsa, za'a tura yan sanda 31,041 jihar Bayelsa, sannan 35,200 zuwa jihar Kogi.

Ya bada tabbacin cewa hukumar ta shirya tsaf domin tabbatar da tsaro a ranan zaben.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Wani gini mai hawa biyu ya rubzo (Hotuna)

Yace: "Hukumar yan sanda a matsayinta na hukumar tsaron da ke kan gaban na tsaron cikin gida ta shirya tsaf wa zaben Bayelsa da Kogi."

"Muna sane da kalubalen tsaro a jihohin nan biyu kuma mun tabbatar dukkan abubuwan da ake bukata na jami'ai da kayayyaki domin dakile rashin tsaro."

"A Bayelsa, zamu tura jami'ai 31.041, sannan mu tura 35,200 Kogi. Wadannan jami'an zasu tsare ko ina a jihohin, babu wani dan daban da za'a bari za hargitsa zabe."

Adamu ya ce hukumar za ta tabbatar da tsaron ma'aikatan INEC da Kayayyakinsu.

Ya ce za'a kare dukkan rumfunan zabe da bankin CBN da aka ajiye kayan zabe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel