Da duminsa: Buhari ya yi ganawar sirri da Yariman Saudiyya, MBS

Da duminsa: Buhari ya yi ganawar sirri da Yariman Saudiyya, MBS

A ranar Alhamis, shugaba Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Yariman Saudiyya mai jiran gado, Mohammed bin Salman, a Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya.

Kamfanin dillancin Najeriya ta bada rahoton cewa ganawar na cikin tattaunawar da shugaba Buhari zai yi kafin tafiya Makkah a yau ta babbar filin jirgin saman sarki Abdulaziz a Jeddah.

A Makkah, shugaba Buhari tare da tawagarda za su gabatar da Ibadar Umrah da Sallan Juma'a a masallacin Harama.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da sarkin masarautar Saudiyya, Sarki Salman, a ranar Laraba, 30 ga watan Oktoba, a Riyadh.

Shugabannin sun tattauna yadda zasu hada kai musamman bangaren arzikin man fetur da iskar gas don cigaba.

Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu, yace: "Shugaban Najeriya da na Saudiyya sunyi yarjejeniya kan yadda masarautar za ta sanya hannun jari a kamfanin man fetur da iskar gas na Najeriya da karfafa hadaka tsakanin Saudi Aramco da NNPC."

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bar Abuja zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na masu saka hannu jari (FII) da hukumar samar da kudaden kasuwanci ta kasar Saudiyyya (PIF) ta shirya.

An fara taron ne daga ranar 29 ga wata kuma za'a kammala ranar 31 ga watan Oktoba, kuma za a tattauna ne a kan harkokin bunkasa kasuwanci ta hanyar fasahar zamani.

A cikin tawagar akwai karamin ministan harkokin kasashen waje, Zubairu Dada, ministan kamfanoni, kasuwanci da saka hannu jari, Niyi Adebayo, karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, da ministan harkokin sadarwa, Dakta Ibrahim Pantami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel