Hawaye sun kwaranya yayinda aka yi jana’izar matar Tafawa Balewa a Bauchi

Hawaye sun kwaranya yayinda aka yi jana’izar matar Tafawa Balewa a Bauchi

Daga karshe an yi jana’izar matar firimiyan Najeriya na farko, Hajiya Jummai Abubakar Tafawa Balewa, wacce ta amsa kiran mahaliccinta a jiya Lahadi, 27 ga watan Oktoba, a jihar Legas.

An binne maigayiyar, Hajiya Jummai a babbar makabarta dake cikin garin Bauchi.

Babban limamin garin Bauchi, Malam Bala Baban-Inna ne ya sallaci gawarta, inda aka yi jana’izar da misalin karfe 2:15 na ranar yau Litinin, 28 ga watan Oktoba, a fadar Sarkin Bauchi.

Hawaye sun kwaranya yayinda aka yi jana’izar matar Tafawa Balewa a Bauchi
Hawaye sun kwaranya yayinda aka yi jana’izar matar Tafawa Balewa a Bauchi
Asali: Facebook

Jana’izar maigayiyar ya samu halartan manyan masu fada aji a kasar, daga ciki harda gwamnan Bauchi, Alhaji Bala Muhammad, Sarkin Bauchi, Alhaji Rilwanu Sulaiman, Sarkin Dass, Alhaji Bilyaminu Usman, sai Sarakunan Ningi, Misau, Katagun, da kuma wakilan Sarkin Jama’are da Yariman Jama’are.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe Liman, sun yi awon gaba da mutane da yawa a Jalingo

Hajiya Jummai a rasu tana da shekaru 85 a duniya, ta bar ‘ya’ya takwas da jikoki masu yawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel