Sanatoci sun kori minista Sadiya Umar Faruk da ta bayyana don kare kasafin kudinta

Sanatoci sun kori minista Sadiya Umar Faruk da ta bayyana don kare kasafin kudinta

Ministan kula da yan gudun hijira da cigaban al’umma, Hajiya Sadiya Umar Faruq ta gamu da cikas a yayin data bayyana gaban majalisar dattawa domin kare kasafin kudin ma’aikatarta na shekarar 2020.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamitin majalisar ta fatattaki Minista Sadiya daga majalisar ne bayan ta bayyana gabansu domin ta kare kasafin kudin, inda shugaban kwamitin, Sanata Lawal Yahaya Gumau yace dalilin fatattakar ministan shi ne rashin mika musu kwafin kasafin kudin ma’aikatan nata na 2019.

KU KARANTA: A karon farko: Najeriya ta fara dinka ma kafatanin jami’an tsaronta khaki a cikin gida

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cikin bakin rai Sanata Gumau ya dinga masifa yana daga murya tare da daura laifin hakan a kan wasu manyan hadiman shugaban kasa guda biyu da suka yi ma Ministar rakiya zuwa majalisar.

“Minista, mun san ke sabuwar zuwa ce, amma wadannan hadiman shugaban kasa guda biyu sun sane da cewa sai an mika mana kasafin kudin 2019 kafin a kawo na 2020. Ina neman afuwan minista, amma banda hadiman shugaban kasa.” In ji Sanata Yahaya Lawal Gumau.

Daga nan Sanatan ya dage cigaba da zaman kare kasafin kudin zuwa ranar Litinin, 28 ga watan Oktoba da misalin karfe 10 na safe, sa’annan ya gargadi ministan data tabbata ta kawo musu dukkanin muhimman takardun da suka kamata.

A nata jawabin, Minista Sadiya Umar Faruk ta nemi gafarar kwamitin saboda rashin mika mata kwafin kasafin kudin 2019, inda ta kara da cewa: “Kwafin kasafin kudin 2020 da muka mika muku yana tare da kasafin kudin 2019 ne amma a cikin na’urar daukan bayanai daga kwamfuta, flash.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel