Gaskiyar lamarin: Yadda mijina ya mutu, Maryam Sanda ta sanar da kotu

Gaskiyar lamarin: Yadda mijina ya mutu, Maryam Sanda ta sanar da kotu

- A jiya ne babban kotun tarayya dake Maitama ta cigaba da sauraron shari'ar Maryam Sanda, wacce ake zargi da kashe mijinta kuma uban 'yarta

- Cikin zubda hawaye ta sanar da alkalin kotun cewa bata taba fatan mijinta ya mutu ba balle ace ita da kanta ta halakasa

- Maryam, ta bayyana cewa fasassar kwalbar Shisha da ta tarwatse yayin da suke rigima da mijin nata ne ta sokesa a kirji

Maryam Sanda da ake zargi da hallaka mijinta Bilyaminu Bello, ta fadi hakikanin abinda ya ja mutuwar mijinta a gaban babban kotun tarayya da ke Maitama, Abuja.

A jiya ne aka cigaba da sauraron shari’arsu. Sanda ta sanar da kotu yayin da take zubda hawaye cewa, duk da akwai matsaloli a auren nata na shekaru biyu, amma ba ita ta kashe mijinta ba.

KU KARANTA: Illar da Fatima Mamman Daura ta yi ga nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ta sanar da kotun cewa, a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2017, ta yi amfani da wayar maigidan nata don yin kira amma bayan nan sai ta ga hoton tsiraicin wata mata a wayar. Ta je wajensa don bukatar karin bayani, amma sai rigima ta sarke tsakaninsu wacce ta kaisu har dare.

Ta bayyana cewa, ta bukaci saki amma sai marigayin ya shaketa. Ta shiga daukan caja dinta amma sai ya tureta har ta fadi kasa. Hakan kuwa yasa ta ture kwalbar Shisha dinsa har ta fashe.

Ya danneni a kasa sai muka ji kukan ‘yarmu. Na rokeshi akan zanje in ga me takewa kuka shine ya sassauta min riko. Yayin da nayi kokarin tashi ne shi kuma ya fadi inda fasassar kwalbar ta sokeshi a kirji,” cewar Sanda.

Na cire masa kwalbar sannan na kira wani Ayuba inda ya taimaka min na kaisa asibiti inda aka ce min ya rasu. Ban aminta ba, hakan yasa na kara kaishi babban asibitin Maitama inda nan ma aka tabbatar min da ya mutu.” fadin Sanda.

"Daga asibitin ne aka kaini ofishin ‘yan sanda inda na rubuta abinda ya faru. Ban kashe mijina ba. Ban taba fatan ya mutu ba,” in ji Sanda.

Ta sanar da kotun cewa, a lokacin da ta nufi asibiti da mijin nata, fasassar kwalbar Shisha din da ruwanta suna nan a falonsu.

Alkalin kotun, Jastis Yusuf Halliru ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Nuwamba inda za a yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel