Kotu ta umarci shugaban hukumar DSS da ya gaggauta sakin Sowore

Kotu ta umarci shugaban hukumar DSS da ya gaggauta sakin Sowore

- Babban kotun tarayya da ke Abuja ta umarci shugaban 'yan sandan farin kaya da ya gaggauta sakin Sowore

- Tun a ranar Laraba Sowore ya cika sharuddan belin da mai shari'a Taiwo Taiwo ya gindaya masa

- Sowore na tsare ne a wajen 'yan sandan tun ranar 3 ga watan Augusta

Babban kotun tarayya da ke Abuja, ta yi barazanar daure babban daraktan 'yan sandan farin kaya, Yusuf Bichi, akan kin bin dokar kotu.

Kotun na zargin hukumar 'yan sandan farin kayan ne akan kin sakin Omoyele Sowore wanda tun a ranar Talata ta bada umarni kuma ya cika sharuddan belin a ranar Laraba.

A wata takardar mai taken "Jawo hankali akan kin bin dokar kotu" da kotun ta mika ta ga shugaban hukumar, ta umarcesa da ya gaggauta bin dokar babban kotun ko ya fuskanci kalubalen da zai dangantasa da gidan maza.

KU KARANTA: Innnalillahi wa inna ilaihirraji'un: Allah ya yi wa wani tsohon kwamishinan lafiya a jihar Kaduna rasuwa

Sowore na tsare a wajen 'yan sandan fiye da sa'o'i 24 bagany da ya cika sharuddan belin da mai shari'a Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayyar da ke Abuja ya gindaya masa a hukuncin ranar Talata.

An kama Sowore a Legas a ranar 3 ga watan Augusta, 2019 da laifin zagon kasa ga mulkin Najeriya da kuma zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel