Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wata budurwa tayi ridda ta koma addinin Kiristanci

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un: Wata budurwa tayi ridda ta koma addinin Kiristanci

- Wata budurwa 'yar kasar Guinea tayi ridda daga addinin Musulunci ta koma addinin Kiristanci

- Budurwar ta bayyana cewa bayan komawrta iyayenta sun nemi ta bar musu gidansu ko kuma su saka a kasheta

- Ta ce hakan ya tilasta ta gudowa Najeriya inda yanzu haka take zaune a wata maboya yayin da 'yan sanda ke nemanta ruwa ajallo

Wata budurwa mai shekaru 20 Musulma 'yar kasar Guinea, mai suna Grace Koulibaly ta wallafa wani rubutu a shafinta na Facebook akan irin barazanar da take samu na kisa bayan komawarta addinin Kiristanci, inda hakan ya tilasta ta gudowa Najeriya daga kasar Guinea.

Budurwar wacce ta samu takardun zama a kasar Amurka ta koma addinin Kiristanci shekaru uku da suka gabata, inda ta ce iyayenta sun dawo kasar Guinea domin yin hutu, inda tayi zargin cewa sunyi hakan ne domin su tilasta ta komawa addinin Musulunci.

Grace ta ce iyayen na ta sun dauke takardun zamanta na kasar Amurka, da kuma duka kudinta, kwanaki uku bayan zuwan su Guinea.

KU KARANTA: Tirkashi: Budurwa ta sha maganin kwari ta mutu, watanni uku bayan saurayinta ya kashe kanshi

Sai dai kuma bayan taki yadda ta koma addinin Musuluncin, iyayentasun bayyana mata cewa ko ta nemi hanyarta daban, ko kuma su saka a kasheta. Grace ta bayyana cewa yanzu haka tana nan ta boye a wani waje a Najeriya yayin da 'yan sanda suke nemanta ruwa ajallo domin mayar da ita kasar Guinea.

Ta bayyana cewa ita ce ta yanke hukuncin gudowa Najeriya babu wanda ya takura ta ko ya sato ta, Grace ta kara da cewa iyayenta sun kai rahoton cewa wani Fasto ne ya sace ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel