'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

'Yan Shi'a sunyi jana'izar mutanen da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

- Musulmi mabiya aqidar Shi'a sunyi jana'izar mutane 4 da suke zargin 'yan sanda da kashe musu

- 'Yan Shi'a sunyi arangama ne da 'yan sandan a harabar babbar kasuwar Bauchi

- Shugaban kungiyar na jihar Bauchi, ya jajanta lamarin ganin cewa sunfi shekaru 20 suna tattaki a kasar nan

A ranar Alhamis din da ta gabata ne musulmi mabiya aqidar Shi'a suka birne mutane 4 'yan kungiyar da suke zargin 'yan sanda da kisansu a Talata a jihar Bauchi yayin tattakin da suka yi a ranar Ashura.

An katse tattakin yayin gamuwar 'yan kungiyar Shi'a da 'yan sanda. An zargi 'yan sandan da harbin wasu daga cikin 'yan kungiyar.

Jim kadan bayan jana'izar da aka yi a filin wasan kwallon kafa na Kobi da ke jihar Bauchi, shugaban kungiyar na jihar, Malam Ahmad Yusuf Yashi, wanda Malam Zilkallaini Aliyu ya wakilta, ya bayyana sunayen wadanda aka kashen da: Uzaifa Adamu, Hussaini Haruna, Uzaifa Sunusi da Ahmed wanda ba a bayyana sunan mahaifinsa ba.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi wa 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka ta Kudu wani kyauta ta musamman

Yace 'yan kungiyar na tsaka da yin tattakin nasu cikin lumana inda 'yan sanda suka fara harbinsu da sukarsu a kusa da babbar kasuwar Bauchi. Hakan ne ya jawo mutuwar mutanen 4.

Yashi ya koka cewa in har za a bar sauran kungiyoyin addini su yi abubuwansu ba tare da hantara ba, toh kuwa bai kamata a dinga hantarar 'yan Shi'a ba.

Kamar yadda ya sanar, sun fi shekaru 20 suna tattaki ba tare ba tare da wani tashin hankali ba, toh kuwa hantarar da ake nuna musu bai kamata ba.

Tun kafin tattakin nasu, 'yan sanda sun ja kunnen 'yan kungiyar akan cewa gwamnati bata yarda da taron nasu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel