Karya doka: An yi won gaba da shahararren mawaki Naziru Ahmad

Karya doka: An yi won gaba da shahararren mawaki Naziru Ahmad

Hukumar tace fina finai ta jahar Kano ta samu nasarar kama shahararren mawakin nan, kuma sarkin mawakan mai martaba Sarkin Kano, Naziru M Ahmad, kamar yadda mujallar Fim ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar ta kama Nazirun ne bisa tuhumar da take masa na sakin wata waka ba tare da tantance wakar ba, kuma ba tare da izininta ba, mai yiwuwa hukumar ta gurfanar da shi gaban kuliya manta sabo a ranar Alhamis, 12 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Jirgin farko na yan Najeriya ya dawo gida daga kasar Afirka ta kudu

Majiyar ta kara da cewa wakar da ake tuhumar da saki ta danganci siyasar zaben gwamnan jahar Kano da aka gudanar a baya, inda sanannen lamari ne cewa Naziru ya bayyana goyon bayansa gad an takarar jam’iyyar PDP, Injiniya Abba Kabir Yusuf Abba Gida Gida.

A yan kwanakin nan hukumar tace fina finai ta yi kamen wasu mutane dake masana’antar Fim na Kannywood irinsu Sanusi Oscar sakamakon zarginsu da yi ma dokokin hukumar karan tsaye.

Shima shugaban kungiyar mawaka, Aminu Alan Waka ya yi tsokace game da cancantar hukumar na tantance wakokin mawaka a cikin wani bidiyo daya saki a jiya, inda yace babu wata hukuma dake da ikon tantance wakokin mawaka.

Sai dai ya kara da cewa amma idan har mawaki ya ci zarafin wani, mutuncinsa, kabilarsa ko addininsa a cikin wakarsa, tabbas ya tsallake layi, kuma akwai dokokin da kundin dokokin Najeriya ta tanadar da za’a iya amfani dasu wajen hukunta shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel