Mahaifiyata ta kasa daukan mataki duk da na fada mata mahaifina na kwanciya da ni - Budurwa

Mahaifiyata ta kasa daukan mataki duk da na fada mata mahaifina na kwanciya da ni - Budurwa

Wata yarinya mai shekaru 14 da aka boye sunanta ta bayyana yadda mahaifiyarta, Uwargida Florence Ifelaka, ta gaza daukan mataki a kan cin zarafinta da mahaifinta ya dinga yi mata.

Matashiyar, wacce aka kai ofishin jami'an hukumar tsaron NSCDC dake Alausa a jihar Legas, ta ce tun tana da shekaru 11 mahaifinta ya fara lalata da ita amma mahaifiyarta bata yi komai a kai ba duk da tana da masaniya a kan abinda ke faru wa.

A cewar matashiyar, hatta a ranar 9 ga watan Agusta sai da mahaifinta ya tilasta mata kwanciya da shi a gidansu dake unguwar Ojo lokacin da mahaifiyarta bata gida.

Ta kara da cewa bayan lokacin ne bata sake ganin jinin al'ada ba, lamarin da yasa ta fara zargin ta dauki juna biyu.

"Sau biyu ya yi lalata da ni lokacin ina da shekaru 11 kuma tun a lokacin na sanar da mahaifiyata amma bata yi komai a kai ba," a cewar matashiyar.

DUBA WANNAN: Mabiya Shia'a fiye da 30 sun mutu sakamakon 'turereniya' yayin tattaki a 'Karbala'

Da aka tambayi matar a kan dalilin da yasa bata dauki wani mataki domin kare diyarta ba, sai ta ce tsoro ne ya hana ta, tare da bayyana cewa mijinta ya yi mata barazanar daukan mataki mai tsauri matukar maganar ta fita waje.

Wata ''yar uwa ga mahifiyar matashiyar ce ta kai wa rundunar NSCDC rahoton abinda ya faru.

Mahaifin matashiyar, Chinedu Ifeleka, mai shekaru 46, ya amsa cewa ya taba lalata da diyar tasa sau daya tare da bayyana cewa sharrin giya ne, bai aikata hakan cikin hayyacinsa ba.

Kwamandan jami'an NSCDC, Cyprian Otoibhi, ya ce tabbas Ifeleka zai fuskanci fushin hukuma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel