Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)

Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)

A yammacin ranar Lahadi, 8 ga watan Satumba, ne dakarun rundunar soji da hadin gwuiwar 'Civilian JTF', maharba da 'Yansakai suka kai wani samame a wata maboyar mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Jami'an hadin gwuiwar sun kai samame maboyar mayakan kungiyar Boko Haram din ne dake kauyen Gworege a karkashin karamar hukumar Dikwa bayan samun sahihan bayanan sirri.

Dakarun sojin sun samu nasarar ragargazar mayakan Boko Haram dake boye a kauyen tare da kwace makamai masu yawa daga hannunsu.

A wata sanarwa da hotuna da ta wallafa a shafinta na Tuwita, rundunar sojin ta ce; "biyo bayan samun sahihan bayanan sirri daga mazauna yankin a kan wata mafakar 'yan ta'adda a kauyen Gworege a karamar hukumar Dikwa, dakarun rundunar ta 22 dake Dikwa tare da hadin gwuiwar mambobin kungiyar 'Yansakai ta farar hula (Civilian Task Force) da 'Yan bijilanti da Maharba sun samu nasarar gudanar da atisaye a wurin.

DUBA WANNAN: Zaben 2019: Mun yi safarar bindigu da makamai ga manyan 'yan siyasa a jihohin arewa uku - Dillalin bindigu

"Dakarun soji sun kai samame mafakar domin fatattaar 'yan ta'addar dake boye a wurin. 'Yan ta'addar sun yi musayar wuta da tawagar dakarun kafin daga bisani su gudu bayan sun ga babu alamun samun nasara."

Kazalika, rundunar sojin ta ce ta gudanar da bincike a kauyen kuma ta yi nasarar samun wasu makamai mallakar 'yan ta'addar da suka hada da; bindigu samfurin AK47 guda 6 da alburusai 66.

Sanarwar ta kara da cewa babu wani soja da ya mutu, ya samu rauni ko kuma ya bata yayin musayar wuta. Sai dai, wani maharbi guda daya ya samu rauni, wanda yanzu haka yana samun kula wa a cibiyar duba lafiyar sojoji dake Dikwa.

Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)
Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)
Asali: Facebook

Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)
Bindigun da aka samu
Asali: Twitter

Rubdugu: Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu (Hotuna)
Sojoji, 'Civilian JTF, maharba da 'Yansakai sun yi wa 'yan Boko Haram kaca-kaca a maboyarsu
Asali: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel