Kasuwar hannun jari ya daga a Najeriya a tsakiyar shekarar 2019

Kasuwar hannun jari ya daga a Najeriya a tsakiyar shekarar 2019

Kasuwar hannun jari a Najeriya ya yi samu riba na kin-karawa a tsakiyar makon nan. Rahotanni sun ce an samu wannan gagarumar riba ne a Ranar Laraba, 21 ga Watan Agusta 2019.

Hannun jari sun yi kasuwar da ba su taba yi ba a cikin watanni biyu inda masu hannun hajoji su ka yi cinikin Naira biliyan 120.7 a kasuwar hannun jarin Najeriya wanda a ka fi sani da NSE.

Jimillar kudin hannun jari ya karu ne da maki fiye da 100 a cikin wannan lokaci. An samu wannan kari ne bayan kamfanin MTN na Najeriya da kuma kamfanin Nestle sun yi wani ciniki.

Bayan kamfanin kayan abincin na Nastle, rahotannin Daily Trust sun nuna cewa babban bankin nan na Ecobank ya yi ciniki a kasuwar hannun jari. Akwai fiye da Tiriliyan 13 yanzu a kasuwar.

KU KARANTA: An ba Najeriya damar karbe gidan Donald Duke a Legas

Hannun jarin da su ka fi kasuwa a Najeriya su ne na bankin UBA, Access, GTB, da Zenith. A wannan jeri ba a bar kamfanin MTN a baya ba, inda miliyoyin hannun jarinsa ke motsawa.

Karfin hannun jarin kamfanonin man fetur ya yi kasa a daidai wannan lokaci. Daga cikin wanda wannan cibaya ya taba akwai kamfanin man Forte Oil wanda ya gamu da rashi har na 0.74%.

Kai-da-komowar da a ke samu a kasuwar ta karu da 13%. Bankuna da kamfanonin kayan abinci irinsu sukarin Dangote da Nestle sun fi samun ciniki a kasuwar hannun jari tsakiyar bana.

Masana tattali sun ce kasuwar hannun jarin ba za ta bude ba a nan gaba kadan. Sai dai a cikin Watan nan Agusta, an samu irin cinikin da a ka yi wata da watanni ba a samu ba ba a fadin kasar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel