Ta fara bayyana: Dalilin da yasa EFCC ke binciken tsohon gwamna Ambode

Ta fara bayyana: Dalilin da yasa EFCC ke binciken tsohon gwamna Ambode

Bayanai sun fara fito wa a kan dalilin da yasa jamai'an hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) suka kai wani samame gidan tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode, ranar Talata.

Jami'an hukumar EFCC sun dira gidan Ambode da ke unguwar Epe da sanyin safiyar ranar Talata amma wasu fusatattun matasa sun hana su shiga gidan.

A wani jawabi da Habib Aruna, mai taimaka wa Ambode a bangaren yada labarai ya fitar, ya ce jami'an na EFCC sun dira gidan Ambode ba tare da wata sanar wa ko aika masa gayyata ba.

Aruna ya kara da cewa jami'an EFCC sun gudanar da bincike a gidan Ambode a lokacin da ba ya Najeriya.

Da ya ke mayar da martani a kan samamen da suka kai gidan tsohon gwamnan, Tony Orilade, kakakin hukumar EFCC, ya ce basu kai samamen da wata manufa ba face gudanar da bincike kamar yadda doka ta basu dama da iko.

"Ba mu yi wani abu da ya saba wa doka ba don mun kai samame gidan Ambode. Ba iya shi kadai muke bincike ba, mu na gudanar da bincike ne a kan dukkan gwamnonin da suka bar mulki tunda yanzu basu da wata kariya da zata hana a gurfanar da su a gaban kotu idan an same su da laifi," a cewarsa.

Sannan ya cigaba da cewa, bisa al'ada, hukumar EFCC ba ta sanar da binciken wani mutum a shafin jaridu.

DUBA WANNAN: Kwatsam: Najeriya ta rufe iyakar ta da Kotono, ta ritsa da dubban 'yan kasuwa

"Cikin sirri jami'an mu ke gudanar da bincike har sai mun kammaa tattara hujjojin da zamu gurfanar da mutum a gaban kotu. A saboda haka, za mu yaki duk wani yunkuri na neman bata sunan hukumar EFCC ta hanyar nuna cewa su na aiki ba bisa doka ba. Aikin mu shine yaki da cin hanci, kuma ba zamu gajiya ba," a cewar Orilade.

EFCC na binciken Ambode ne a kan zarginsa da tafka almmubazzaranci da kudin jama'a a lokacin da ya mulki jihar Legas daga shekarar 2015 zuwa 2019. Bayan zarginsa da yi wa tattalin arzikin jihar Legas rashin adalci a karkashin wani aiki 'Visionscape', EFCC na zargin Ambode da bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba.

Wata majiyar EFCC ta bayyana cewa ana binciken alakar Ambode da wani banki a tsawon shekaru hudu na mulkinsa. Sai dai, duk wannan bincike da ake yi a kansa, Ambode ya fice zuwa Landan, kasar Ingila, kuma babu wanda ya san ranar dawowarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng