Kiwon Lafiya: Illoli da kuma amfanin tsamiya a jikin dan Adam

Kiwon Lafiya: Illoli da kuma amfanin tsamiya a jikin dan Adam

Tsamiya na daya daga cikin dangin ‘ya’yan itatuwan da al’ummar Hausawa musamman a Najeriya da kuma mutanen birnin Sin ke amfani da su sosai a rayuwar su ta yau da kullum.

Ta na kunshe da sunadarai kamar haka: Magnesium, Potassium, Iron, Calcium, Phosphorus, Vitamin B1 (thiamin), Vitamin B2 (riboflavin), Vitamin B3 (niacin), vitamin C, vitamin K, vitamin B6 (pyridoxine), folate, vitamin B5 (pantothenic acid), copper da kuma selenium.

Tsamiyar tana tasirai masu tarin yawa ta fuskar inganta lafiya, haka kuma tana wasu illoli idan aka sha ta ba bisa ka’ida ba. Ana amfani da tsamiya wajen sarrafa abubuwan sha, wajen yin magani, da kuma a girke-girke a matsayin abun karin dandano.

Ga wasu jerin matsaloli da tsamiya ke magancewa a jikin bil Adama kamar haka:

1. Cushewar ciki da rashin yin bahaya

2. Mura da zazzabi

3. Ciwon ciki

4. Tashin zuciya ga masu ciki

5. Tsutsar ciki

6. Matsolin da suka shafi hanta da madaciya

7. Tana wanke dattin ciki da kuma cushewar hanji

8. Ana amfani da ganyenta wajen magance cutukkan daji (cancer)

9. Ana tafasa ruwanta ayi wanka dasu dan magance ciwon gabobin jiki.

10. Tana sanya cin abinci domin kuwa tana sanya saurin jin yunwa

Illolin amfani da tsamiya sun hadar da:

1. Tsamiya za ta iya haifar da illa ga masu ciwon sukari saboda tana rage adadin sukarin da ke cikin jini. Haka ma ga wadanda za a yi wa tiyata, ana so su dakatar da shan tsamiya akalla makonni biyu kafin a yi aikin tiyatar saboda wannan dalili.

KARANTA KUMA: Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin dan Adam

2. Ga ramammu, yawan shan tsamiya na iya kara rama. Ga masu kiba kuwa za ta taimaka masu wajen rage kiba

3. Ba a son a sha tsamiya da magungunan Ibuprofen da Aspirin saboda ta na kara adadin su da ke shiga jini. Idan haka ya faru, magungunan ka iya yin yawa su haifar da matsala.

4. Shan tsamiya a kai a kai yana rage karfin sha'awar namiji.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel