Sakon sarkin Zazzau ga shuwagabanni: Mutanenmu na shan bakar wahala

Sakon sarkin Zazzau ga shuwagabanni: Mutanenmu na shan bakar wahala

Mai martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Dakta Shehu Idris ya yi kira ga shuwagabanni a matsakin jaha da gwamnatin tarayya dasu sama ma jama’a sauki daga cikin wannan kangin rayuwa da suka fada.

Sarkin ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar da jawabinsa na barka da Sallah a fadarsa dake birnin Zazzau, inda ya nemi gwamnatoci a dukkanin matakai dasu jajirce wajen kula da walwalar yan Najeriya.

KU KARANTA: Tabbatar da zaman lafiya da sauran sakonni 6 da Buhari ya yi a jawabansa na goro Sallah

“Ya kamata gwamnatoci su waiwayi yan Najeriya su tallafa musu wajen fita daga cikin bakar wahalar da suke fama da shi, haka zalika suma mutane muna kira garesu dasu daure wajn zaman lafiya da junansu, makiyaya da manoma su girmama juna, jama’a su daina watsa jita jita kuma su baiwa jami’an tsaro hadin kai.

“Gwamnatin jahar Kaduna, ta kananan hukumomi da majalisar dokokin jahar Kaduna su dauki matakan samar da cigaba ta bangaren noma, kiwo da kuma ilimi, idan har aka samu haka, zasu samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma tare da inganta rayuwarsu.” Inji shi.

Haka zalika, Sarkin ya yi kira ga gwamnati da ta taimaka ma manoma wajen sayan amfanin gonarsu domin su samu riba, sa’annan ya yi kira ga jama’a su gaggauta sanar da hukuma wanzuwar duk wasu cututtuka a yankunansu.

Daga karshe Sarkin ya nemi iyaye su dinga sanya idanu a kan yayansu domin hanasu fadawa halin ta’ammali da shan miyagun kwayoyi, wanda a yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin matasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel