Mijina mazinaci ne, ya dirka ma babbar kawata ciki – Uwargida ta shaida ma kotu

Mijina mazinaci ne, ya dirka ma babbar kawata ciki – Uwargida ta shaida ma kotu

Babbar kotun gargajiya dake zamanta a garin Mapo na birnin Ibadan, babbar birnin jahar Oyo ta saurari wata bahallatsa data kunno kai tsakanin wasu ma’aurata, Sherif Adesola da matarsa Damilola.

A yayin zaman kotun na ranar Alhamis, 8 ga watan Yuli, Sherif ya bayyana ma kotu cewa ta yi gaggawar raba aurenshi da Damilola sakamakon tana da nufin kasheshi ko ba jima ko ba dade, sa’annan kuma tana neman maza.

KU KARANTA: Uwargidar gwamna ta fara horas da yan mata fadar Taekwando don yaki da fyade

Sheriff ya tabbatar ma kotu cewa shi da idonsa ya kama Damilola tana barbada masa guba a cikin abinci a lokacin da ya nemi ta kawo masa abinci ya ci, kuma koda ya kai kararta ga iyayenta basu dauki wani kwakkwaran mataki ba.

“Damilola na da halin neman rigimana a cikin jama’a, tana zazzagina a bainar jama’a, don haka ku taimaka ku raba ni da ita kafin ta kasheni.” Inji shi.

Sai dai ita ma Damilola ta amince ma kotun ta raba aurenta da Sheriff saboda a cewarta Sheriff mazinaci ne na kin karawa, wanda har ta kai gay a dirka ma babbar kawarta ciki, daga baya asirinsu ya tonu.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, Alkalin kotun, Cif Ademola Odunade ya bayyana ma ma’auratan cewa dangantaka tsakaninsu ta yi tsami kuma ba za ta taba gyaruwa ba, don haka ya yanke hukuncin kashe auren nasu.

Sai dai Alkali Odunade ya mika yaran ma’auratan guda biyu ga uwargida Damilolo, sa’annan ya umarci mahaifinsu Sheriff ya dinga biyan Damilola kudi naira dubu biyar biyar a duk wata don kulawa da yaran.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel