Yadda kishi ta tunzura wani ya harbe saurayin wata budurwa da ya ke kauna

Yadda kishi ta tunzura wani ya harbe saurayin wata budurwa da ya ke kauna

Wasu mutane biyu sun kashe wani matashi mai shekaru 24 a ranar Juma'a a kauyen Umuru da ke karamar hukumar Idemili ta Arewa na jihar Anambra kan rikicin budurwa.

An ruwaito cewa wanda ake zargin, Dubem Okeke mai shekaru 28 yana son wata budurwa Ifenyichukwu Kamsisichukwu wacce marigayin ke soyaya da ita.

The Nation ta ruwaito cewa an gano Dubem ya hada baki da abokinsa Okechukwu Okafor ne wurin kashe marigayin.

A cewar majiyar, wanda ake zargin ya tafi gidan marigayin da bindiga a hannunsa tare da abokinsa inda ya harbe shi nan take ya mutu.

DUBA WANNAN: Hotunan sabbin wurare masu ban al'ajabi a duniya

"Yayin da Dubem ya ji labarin cewa marigayin yana gida Kamsi, ya garzaya gidan tare da abokinsa Okechukwu ya shiga dakin da suke ya kuma harbe shi da bindiga," a cewar majiyar.

Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce tuni 'yan sandan Ogidi sun kama wadanda ake zargin.

Ya ce an gano bindigar da akayi amfani da ita wurin kashe marigayin a hannun su.

Ya ce, "Wadanda ake zargin sun tafi gidan Ifenyichukwu Kamsisichukwu mai shekaru 20 suka tilasta mata bude kofar dakin ta kuma suka fita da saurayin ta Chinedu Okoye waje suka harbe shi da bindiga.

"Yan sanda sun ziyarci inda abin ya faru inda suka garzaya da wanda aka harba a baya zuwa asibitin Twinke da ke Ogidi.

"Daga bisani likita ya sanar da cewa ya rasu yayin da ke kan yi masa magani."

Mohammed ya ce an ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki na asibitin Iyienu da ke Ogidi domin gudanar da binciken sanadin mutuwarsa yayin da ake cigaba da bincike kan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel