Kannywood: Yadda fim din barkwanci mai suna Wakili ya samu karbuwa a sinima

Kannywood: Yadda fim din barkwanci mai suna Wakili ya samu karbuwa a sinima

Shahararren fim din nan na barkwanci wanda mutane suka dade suna zuba idon gani na kan nunawa a sinima, sannan fim din ya samu karbuwa sosai a wajen masoya kallon fina-finan Hausa na Kannywood a kullun.

Da yake Magana da manema labarai bayan kallon wasan, Dr. Shamsuddeen Mai Yasin ya nuna jin dadi kan fim din barkwancin inda ya bayyana shi a matsayin wasan barkwanci na Hausa da ya cancanci samun lambar yabo.

A cewarsa, wasa ne da aka yi shi da sigar barkwanci amma akwai sakonni da jawabai da dama tattare dashi tare da darasi mai amfani sosai.

Wasan na kunshe da manyan jarumai irinsu Ali Nuhu, Sulaiman Bosho, Rabi’u Daushe, Hadiza Gabon, Aminu Momo,Falalu A Dorayi.

Wakili ya kasance fim din bakwanci na Hausa da ke nuna al’adu da dabi’un wasu shugabannin al’umma yayinda suke gudanar da ayyukan da ya rataya a wuyansu. Ya kuma nuna yadda tsarauta take ta sigar barkwanci domin nishadantar da masoya.

KU KARANTA KUMA: Kotun zaben Shugaban kasa: Yadda jami’in INEC ya karbi $10,000 - Shaida

An tattaro cewa an shirya fim din ne wanda Darakta Falalu A Dorayi ya shirya tare da hadin gwiwar masarautar Zaria karkashin jagoranin mai martaba Alhaji Shehu Idris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel