Miyetti Allah ta karyata bidiyon da aka ga ana ma Fulani korar kare a Enugu

Miyetti Allah ta karyata bidiyon da aka ga ana ma Fulani korar kare a Enugu

-Wani bidiyo na ta yawo a yanar gizo inda aka ga wasu mutane na korar makiyaya da ake zargin cewa Fulani ne tare da shanunsu

-Amma rundunar yan sanda da kungiyar Miyetti Allah sun karyata ingancin bidiyan

-Amma wasu yan kauyen sun bayyana cewa sun gaji da irin wulakancin da Fulani ke masu inda suka bayyana cewa sunyi asara fiye da N10.9m saboda Fulani

Kwannan ne wanin hotan bidiyo ya yadu a yanar gizo inda aka ga wasu mutane da ake zargin cewa al’ummar garin Agbada Nenwe ne dake a karamar hukumar Aninri dake jihar Enugu suna korar wasu makiyaya da ake tunanin Fulani ne tare da garken shanunsu mai yawa.

Rundunar yan sanda da kungiyar Miyetti Allah sun karyata wannan bidiyan inda suka ce babu wani abu makamanci hakan da ya faru. Amma binciken jaridar Punch ya tabbatar da cewa an samo wannan bidiyan ne daga kauyen.

Wasu mutane yan asalin kauyen da suka zanta da jaridar Punch sun tabbatar da gaskiyar bidiyan na yanar gizo dake nuna wasu matasa suna korar makiyaya da dabbobinsu kuma suna bayyana dalilinsu na aika hakan.

Amma alamu sun suna cewa an gargadi yan kauyen akan cewa suyi gum da bakinsu game da lamarin, amma wasu daga cikinsu sun bayyana irin asarar da sukayi a hannun Fulani a shekaru hudu da suka wuce.

Sun kai dan jaridar na Punch wasu gonakkinsu inda suka bayyana cewa sun bar gonakin haka nana basu noma ba saboda kiwon da makiyaya ke yi a cikin gonakin, inda kuma suka bayyana cewa basu san makiyayan su kara dawo wa.

Sun bayyana cewa suna bin makiyayan kudi Naira miliyan 10.9 na hatsin su da dabbobin makiyayan suka cinye a wasu gonaki masu yawa.

Rundunar yan sanda ta jihar ta bayyana ta bakin mai magana da yawun rundunar, Ebere Amaraizu cewa wannan bidiyan ba gaskiya bane.

Rundunar ta kara da cewa sun fara bincike don gano tushen wannan bidiyan don a kama wadanda suka yada shi su fuskanci hukunci.

KARANTA WANNAN: Kotun zaben shugaban kasa: Atiku ya gabatar da hujjoji 26,000 don tabbatar rinto akayi masa

Da yake musanta lamarin, shima gwamnan jihar, Ifeanyi Ugwuanyi ya yi kira ga makiyaya da al’ummar kauyen da su zauna lafiya da juna. Gwamnan ya ziyarci kauyen a ranar Litinin 1 ga watan Yuli 2019 inda ya bayyana cewa jihar Enugu jihar zaman lafiya ce kuma jihar kowa da kowa ce.

Shugaban gargajiya na kauyen, Igwe Francis ya bayyana cewa abinda ya faru a ranar 29 ga watan Yuni 2019 ba za a kwatanta shi da korar Fulani daga kauyen ba.

Da yake maida jawabi, shugaban Miyetti Allah na yankin, Alhaji Gidado Siddik ya bayyana bidiyan a matsayin wani abun da ke son ya kawo rudani.

Amma wani dan kauyen da ya bayyana kanshi a matsayin Obinna Ofudo ya ce barnar da Fulani ke yi a garin tsawon shekaru hudu ba ta misaltuwa.

Ya bayyana cewa “ Ta ya za ayi ace kana kwashe shinkafar da koma kawai sai makiyayi ya zo da shanunsa cikin gonarka ya na ce maka kayi sauri ka gama saboda shanunsa su yi kiwo. Idan ko wani abu ya sanya baka gama kwashewa ba a ranar, to sai dai ka zo ka tarar shanun sun cinye hatsin.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel