Allah ya kyauta: Wata mata ta haukace jim kadan bayan ta fallasa cewa da ruwan makabarta take dafa abincin sayarwa

Allah ya kyauta: Wata mata ta haukace jim kadan bayan ta fallasa cewa da ruwan makabarta take dafa abincin sayarwa

Babu shakka abubuwan ban mamaki da al’ajabi na faruwa a fadin duniya, wasu na faruwa ne saboda son zuciya da kwadi, da kuma tsananin don kudi ta kowani yanayi.

Hakan ce ta kasance akan wata mata yar jihar Akwa Ibom wacce ke da wajen siyar da abinci, inda ta haukace yayinda take a gidan siyar da abincinta wanda ke a yankin Aleto a karamar hukumar Eleme na Port Haurcourt, jihar Rivers.

Rahotanni sun nuna cewa ba tare da bata lokaci ba matar ta fara hauka tuburan, inda ta yaga kayayyakin jikinta sannan ta fara fallasa wasu ayyukan assha da ta aikata.

Ta kuma fallasa yadda ta yi asiri domin habbaka da bunkasa kasuwancinta na siyar da abinci.

Da take bayyana mugun asirin da tayi, matar tace tana gauraya ruwan da aka yi ma gawa wanka cikin abincinta. Haka zalika ta bayyana cewa tana zuba ruwan da ta wanke gabanta da jinin haila cikin abincin da take siyarwa.

Har ila yau matar ta bayyana cewa tana aikata dukkanin wadannan abubuwa ne domin janyo hankalin abokan ciniki wanda take amfani da “tauraronsu”wajen bunkasa kasuwancinta da kuma samun arziki mai yawa.

KU KARANTA KUMA: Kuji abin al'ajabi: Wasu tagwaye sun mutu a daidai ranar da aka haifesu, kuma cikin irin yanayin da aka haifesu

Daga nan sai tana ta guje-guje tsirara, tana ci gaba da fallasa abubuwan da tayi wanda ke tabbatar da haukarta tuburan.

Labarin abubuwan da take aikatawa ya bazu a yankin inda wasu daga cikin masu siyan abincinta ciki harda yan achaba suka far mata da duka, kafin jami’an yan sanda su cece ta inda suka tafi da ita.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel