Rikicin raban gadon Marigayi sanata Usman Albashir

Rikicin raban gadon Marigayi sanata Usman Albashir

- A yau Laraba 19 ga wayan Yuni ne aka cigaba da sauraren rikicin raba gadon Marigari sanata Albashir

- A zaman na yau, wani Isah Bello ya gabatar da shaidarsa inda ya bayyana cewa bai san sanata Abashir da wasu ya'ya ba bayan ya'yansa guda bakwai da ya bayyana ma kotu

-Ya kuma bayyana ma kotun cewa gamayyar kamfanonin Savannah mallakin mamacin ne

A cigaba da sauraren kara kan rikicin gadon marigayi sanata Usman Albashir, wani Isah Bello a yau Laraba 19 ga watan Yuni 2019 ya shaidawa kotun da ke gudanar da shari’ar cewa marigayin ya rasu ya bar ya’ya na cikinsa guda bakwai da kuma mata daya.

Matar marigayi Albashir ta shigar da kara ta hannun lauyanta, Ayoola Oke, inda ta bukaci kotu ta umurci a raba gadon mijinta a tsakanin ya’yanshi kamar yadda shari'ar musulunci ta tsara.

Isah Bello, wanda lauya ne kuma abokin mamacin, ya kara gaya ma kotu cewa shi kanshi ya san mamacin na da kadarori bakwai a Abuja kadai.

KARANTA WANNAN: Riciki ya salwantar da rayukan mutanen Najeriya 25,794 a wa'adin gwamnatin Buhari na farko - Bincike

Da aka tambaye shi ko yasan cewa mamacin na da wasu magada, sai ya fadawa kotu cewa baida masaniya

Ya ce “Abinda kawai nasani shine wadannan ya’ya bakwan da na zayyana a baya da kuma matarsa ma’aikaciyar asibiti.”

“Ban sani ba ko a wani lokaci ya taba samun wani iyalin”

Ya kuma kara da cewa kanen mamacin wanda shike kula da kadarorin mamacin a Abuja, ya mika lamarin zuwa ga bangaren sasanci na kotun daukaka kara ta shari’ar musulunci.

Ya kara da cewa marigayin ne ke da mallakin gamayyar kamfanin Savannah wanda a cikinsa akwai kamfanoni guda biyar.

Da yake musanta shaidar Isah Bello, lauyan wanda ake kara, Mohammad Sani, ya bukacin kotun da tayi watsi da shaidar inda ya kara da cewe shaidar shashi fadi ce.

Amma Alkalin, Ado Mukhtar ya karbi sahaidar inda ya ce “A shari’ar musulunci, akwai wurare shida da za’a iya karbar shedar shashi fadi. Daya dada ciki ko shine wajen maganar gado idan shaidar tayi daidai da bayanan da kotu ta tattara.”

Alkalin ya dage shari’ar zuwa 1 ga watan Yuli na shekarar 2019 don cigaba da sauraren shari’ar.

Sanata Albashir wanda ya wakilci Yobe ta arewa kuma yayi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP a shekarar 2011, ya rasu a ranar 3 ga watan Yuli 2012 sakamakon hadarin mota da ya gamu dashi a tsakanin hanyar Kano zuwa Zariya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel