Cikin Hotuna: Gwamna Bello da tawagar sarakunan jihar Kogi sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

Cikin Hotuna: Gwamna Bello da tawagar sarakunan jihar Kogi sun ziyarci shugaba Buhari a fadar Villa

A yau Laraba 19, ga watan Yuni, shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin fadar sa ta Villa dake garin Abuja, ya karbi bakuncin tawagar sarakunan gargajiya na jihar Kogi bisa jagorancin gwamnan jihar, Yahaya Bello.

Shugaban kasa Buhari ya karbi bakuncin tawagar sarakunan gargajiya bisa jagorancin mai martaba sarkin kabilar Igala, Attah Igala Michael Idakwo da sauran sarakunan gargajiya tare da gwamnan jihar Yahaya Bello.

Gwamna Bello da tawagar sarakunan jihar Kogi yayin ziyartar shugaba Buhari a fadar Villa
Gwamna Bello da tawagar sarakunan jihar Kogi yayin ziyartar shugaba Buhari a fadar Villa
Asali: Facebook

Hadimin shugaban kasa a shafinsa na Facebook, Buhari Sallau, ya ce tagawar jagororin jihar Kogi ta ziyarci fadar shugaban kasa da manufa daya ta mika gaisuwa da yiwa shugaba Buhari son barka yayin ci gaba da riko da akalar jagorancin kasar nan.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan jaridar Legit.ng ta ruwaito, gwamnonin jam'iyyar APC a ranar Talata da gabata sun ziyarci shugaba Buhari a fadar sa ta Villa, inda suka tattauna a kan batutuwan zaben majalisar Tarayya, tattalin arziki, tsaro da kuma riko da gaskiya.

KARANTA KUMA: Riciki ya salwantar da rayukan mutanen Najeriya 25,794 a wa'adin gwamnatin Buhari na farko - Bincike

Gwamnan jihar Kebbi da ya kasance shugaban kungiyar gwamnonin APC, Abubakar Atiku Bagudu, shi ne ya bayar da wannan shaida yayin ganawar sa da manema labarai na fadar shugaban kasa.

Kazalika gwamna Bagudu ya kungiyar gwamnonin ta yaba da kwazon gwamnatin shugaban kasa Buhari akan harkokin bunkasa noma, inganta albashin ma'aikata, fansho da kuma kudaden sallama daga aiki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel