Wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dangane da matar shugaban kasa Aisha Buhari

Wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani dangane da matar shugaban kasa Aisha Buhari

- Aisha Buhari kwararriya ce a bangaren ado da kwalliya

- Haka kumaa ta kware a fannin gyaran fata wato mai da tsohuwa yariya

- Ta yi yawancin karatun ta a kasar Birtaniya da Faransa

Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ita ce uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, uwar gidan shugaban kasar ta kware matuka a bangaren ado da kwalliya, sannan kuma kwararriyar marubuciya ce.

Kafin ta soma karatun digiri dinta, Aisha ta shiga cikin sana'ar ado da kwalliya a zamanance, inda har taje ta karanci wannan bangare a makaranta.

Ta samu sakamako na difloma a bangaren ado da kwalliya a Jami'ar Carlton Institute of Beauty Therapy, dake kasar Birtaniya, a jami'ar ne ta samu kwarewa matuka a tsara kwalliya ta zamani, sannan ta karo ilimi a bangaren kula da fata, ma'ana mai da tsohuwa yarinya.

KU KARANTA: Wata sabuwa: An bankado yadda Sarki Sanusi ya karkatar da naira biliyan 3.4 na masarautar Kano

Kafin shugaban kasa Buhari ya hau mulki a shekarar 2015, Aisha ta bude wani babban shago na kwalliya da yiwa mutane tausa mai suna Hanzy Spa, sannan kuma ta bude makarantar koyar da kwalliya mai suna Hanzy Beauty Institute a Abuja da kuma garin Kaduna.

Aisha ta samu shaidar kammala difloma a bangaren ado da kwalliya a kwalejin Academy Esthetique Beauty Institute dake kasar Faransa. Haka kuma ta zama mamba a kungiyar koyar da sana'ar hannu dake alaka da ado, kwalliya da kuma kiwon lafiya ta kasar Birtaniya.

Bayan hawan mijinta kujerar shugaban kasa ta rufe shagonta na Hanzy Spa da kuma makarantarta ta Hanzy Beauty Institute.

Haka kuma Aisha ta wallafa wani littafi mai suna: "Essentail of Beauty Therapy: A Completw Guide for Beauty Specialists" wanda a yanzu haka ake amfani dashi a NBTE.

Sannan kuma Aisha ta kasance mai kokarin kare hakkin dan Adam da kananan yara, inda take kokarin ganin kowacce 'ya ta mace ta samu akalla ilimin makarantar firamare da kuma na sakandire kafin ayi mata aure, sannan kuma take kokarin ganin ta hana aurar da mace wacce ba ta kai shekaru 17 a duniya ba.

Aisha ta na da 'ya'ya guda biyar da kuma jika guda daya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel