Hukumar Kwastam ta fara gwanjon Motoci a shafin yanar gizo
Kamar yadda ta saba lokaci bayan lokaci, hukumar hana fasakauri ta Najeriya, ta sake da bujuro da kakar gwanjon hajoji domn sayar wa da mabukata cikin rahusa ta hanyar wani sabon shafi da ta kirkira a yanar gizo.
Hukumar Kwastam za ta yi gwanjon kayayyaki da ta kwace a hannun 'yan sumoga kama daga motoci na alfarma da kayayyaki daban daban musamman a rassan ta na jihohin Imo, Abia, Edo da kuma Delta.
Babban jami'in hukumar na reshen jihar Imo, Kwanturola Kayode Olusemire, shi ne ya bayar da shaidar hakan yayin ganawar sa da manema labarai na jaridar Daily Trust cikin birnin Benin a ranar Laraba.
Kwanturola Kayode da yake fashin baki dangane da yadda gwanjon hajojin zai kasance, ya bayyana cewa hukumar za ta yi gwanjon kayayyaki da dama cikin rahusa ga mabukata a ranar Litinin da kuma Laraba har na tsawon wata guda ta hanyar yanar gizo.
KARANTA KUMA: Hanyoyi 8 na kauce wa fadawa hannun masu garkuwa da mutane
A cewar sa, mabukata dake neman samun mallaki Mota ko kumu wasu kayayyaki na more rayuwa ka iya shiga shafin yanar gizon ta na app.trade.ng/eauction domin zabin hajar da suka bukata daidai da tanadi na hukumar.
Kwanturola Kayode ya ce cikin ire-iren motoci na alfarma da hukumar za ta yi gwanjon su a wannan lokaci sun hadar da Rolls Royce, Mercedes, Toyoto da kuma nau'ikan motocin zamani daban daban na kece raini.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:
https://fb.gg/play/ramadan_ramadan
Asali: Legit.ng