Laifin gwamnati ne matsalar tsaron Najeriya - PDP

Laifin gwamnati ne matsalar tsaron Najeriya - PDP

Babbar jam'iyyar adawar Najeriya wato jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa rikicin da ake ta faman fuskanta a kasar nan ta fannin tsaro ya na da nasaba da yadda gwamnatin shugaba Buhari ke gabatar da mulkin ta

Sanata Umaru Tsauri, sakataren jam'iyyar PDP na kasa shine ya bayyana hakan ga manema labarai a wata hira da yayi da su.

Ya ce rashin bayyanawa al'umma gaskiyar abinda ke faruwa a kasar nan da gwamnati take yi shine ummul aba'isin abinda ya jefa kasar cikin halin ha'ula'i na rashin tsaro.

Ya ce "Gwamnati ce ta janyo wannan matsalar saboda taki fitowa ta bayyana mutane gaskiyar abinda ke faruwa domin daukar mataki."

Laifin gwamnati ne matsalar tsaron Najeriya - PDP
Laifin gwamnati ne matsalar tsaron Najeriya - PDP
Asali: Twitter

Ya kuma kara da cewa alhakin gwamnatin kasa ne ta gano mutanen da suke da hannu a matsalar tsaro a kasar nan, ba wai al'ummar kasa ne za su gano mata ba.

Sanatan ya ce halin da Najeriya ta ke ciki su kansu 'yan jam'iyyar adawa yana damunsu matuka, saboda matsala ce da ta shafi kowa da kowa a kasar nan.

Ya bayyana cewa mafita daya ce yanzu, shine gwamnati ta shawo kan matsalar wurin binciko masu hannu a matsalar tsaron, sannan ta yarda cewa matsalace babba, kuma ta nemi mafita ta hanyar amfani da taimakon manyan mutanen da ke cikin gwamnati.

KU KARANTA: Jihohi da yawa za su talauce idan aka fara biyan sabon albashi

"A ko yaushe gwamnati ta na nuna cewa matsalar tsaro ba ta kai yadda ake tunaninta ba, saboda kullum talakawa abin yake shafa, kuma sune ake yin garkuwa da su," in ji Sanatan.

Ya ce duk lokacin da aka sace wani babban mutum a kasar nan gwamnati ba ta sakin jiki, saboda haka mene zai hana a dinga bin hanyar da aka bi aka kwato wancan babban ita ma abi ta a kwato talakawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel