Yanzu Yanzu: Kungiyar gwamnonin arewa sun zabi shugaba, za su kafa wata kwamitin hadin gwiwa

Yanzu Yanzu: Kungiyar gwamnonin arewa sun zabi shugaba, za su kafa wata kwamitin hadin gwiwa

- Kungiyar gwamnonin arewa sun yi zaben sabon shugabansu a yau Juma'a, 17 ga watan Mayu

- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ne yayi nasarar hayewa wannan kujera bayan ya samu goyon baayan takwarorinsa

- An gudanar da zaben sabon shugaban ne a jihar Kaduna, a taron farko da kungiyar tayi a wannan shekarar

- Gwamnonin sun kuma yanke shawarar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matsalolin tsaro a yankin

Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya zama shugaban kungiyar gwamnonin arewa na wasu shekaru hudu masu zuwa.

Takwarorinsa ne suka zabe shi a lokacin taron kungiyar gwamnonin arewa wanda ya gudana a Kaduna a ranar Juma’a, 17 ga watan Mayu.

A wajen taron wanda shine na farko a shekarar nan, gwamnonin sun amince da kafa wani hukumar kudi na hadin gwiwa wanda zai taimaka wajen kawo ci gaban al’umma da tattalin arziki a yankin sannan hakan zai bayar da damar dogaro da kai ta bangaren kudi.

Yanzu Yanzu: Kungiyar gwamnonin arewa sun zabi shugaba, za su kafa wata kwamitin hadin gwiwa
Yanzu Yanzu: Kungiyar gwamnonin arewa sun zabi shugaba, za su kafa wata kwamitin hadin gwiwa
Asali: Facebook

Gwamnonin sun kuma yanke shawarar ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan matsalolin tsaro a yankin.

KU KARANTA KUMA: Lalong ya kwaikwayi Ganduje, ya kasafta masarautar Jos

Ana sanya ran ganawar gwamnonin wanda daga bisani ya shiga sirri, zai samu jawabai akan yanayin tsaro a fadin jihohin da kuma sadaukarwa daga jami’an kamfanin ci gaban arewacin Najeriya kan nasarorin da aka samu a fannin hako mai a tafkin Chadi, da kuma farfado da durkusashen kamfanin buga kayayyaki na Kaduna mallakar jihohin arewa 19.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel