Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa

Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa

Wata yarinya 'yar kasar Malaysia mai shekaru 16 a duniya ta kashe kanta bayan ta wallafa rubutu a shafinta na Instagram, inda take tambayar abokanta da su zaba mata tsakanin mutuwa da rayuwa

A cewar hukumar 'yan sandan kasar ta bayyana cewa, sama da kashi 69 cikin dari ne suka yi mata zabin ta kashe kanta. Yarinyar ta sanya rubutun a shafinta na Instagram da misalin karfe 3 na yamma, ranar 13 ga watan Mayu, 2019, inda ta yi rubutun na ta kamar haka: "Dan Allah ku taimake ni ku ta ya ni zabi tsakanin mutuwa da rayuwa, bayan sa'o'i biyar sai aka sameta a mace.

Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa

Wata yarinya ta kashe kanta bayan ta nemi abokanta na Instagram su taya ta zabi tsakanin mutuwa da rayuwa
Source: Facebook

Wasu mutane sun yi tambayar ko hukuma za ta kama wadanda suka zaba mata mutuwar a matsayin wanda suka kashe ta. Zuga mutum ya kashe kansa ba karamin laifi bane a kasar Malaysia, inda ake yanke hukuncin kisa ko kuma shekaru ashirin a gidan yari ga duk wanda ya aikata irin laifin.

Wani lauya mai suna Ramkarpal Singh, ya bukaci hukumar tsaro da ta gabatar da bincike akan lamarin. "Da ace abokan nata basu zaba mata mutuwa ba da yanzu haka tana nan da ranta," in ji shi.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta tabbatar da Godwin Emefiele a matsayin gwamnan babban banki karo na biyu

Ching Yee Wong, shugaban kamfanin sadarwar Instagram, ya bayar da wannan sanarwar ga wata jarida a lokacin da ya ke amsa tambayoyi game da mutuwar yarinyar:

"Muna mika ta'aziyyar mu ga iyalan wannan yarinyar, sannan muna taya ta addu'ar rabauta. Mu muke da alhakin tabbatar da cewa mutanen da suke amfani da Instagram suna zaune lafiya ba tare da wata barazana ga rayuwarsu ba. Muna rokon mutane da su yi gaggawar sanar damu idan har suka ga wani mutum ya wallafa abu makamancin haka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel