Labari mai dadi: Hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara za su dauki ma'aikata dubu 10

Labari mai dadi: Hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara za su dauki ma'aikata dubu 10

- Gwamnatin tarayya ta bai wa hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara umarnin daukar ma'aikata kimanin dubu goma a fadin kasar nan

- Hukumomin sun bada sanarwar cewar za su sanar da al'umma da zarar sun gama shirin daukar ma'aikatan

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta umarci Hukumar Gidan Yari da Hukumar kashe gobara ta kasa akan su dauki ma'aikata 9,675 a Najeriya.

Yayin da hukumar gidan yari za ta dauki ma'aikata 7,475, ita kuma hukumar kashe gobara za ta dauki ma'aikata guda 2,200.

Gwamnatin tarayya ce ta umarci hukumomin biyu akan su dauki ma'aikatan.

Labari mai dadi: Hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara za su dauki ma'aikata dubu 10
Labari mai dadi: Hukumar gidan yari da hukumar kashe gobara za su dauki ma'aikata dubu 10
Asali: UGC

A wata sanarwa da aka fitar ranar Talata a Abuja, wacce sakataren hukumomin, Al-Hassan Yakmut ya sanyawa hannu, ya ce shugaban hukumomin shine ya bada umarnin daukar ma'aikatan a wurin wani taro da aka gabatar a Abuja ranar 9 zuwa 10 ga watan Mayu.

Ba a bayyana ainahin ranar da za a fara gabatar da daukar ma'aikatan ba.

KU KARANTA: Abinda ake gudu ya afku: Zirga-zirga ta ragu a fadar sarkin Kano

Taron wanda ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya shugabanta, ya yadda da cire banbanci tsakanin masu rike da kwalin digiri da kuma na HND a hukumomin wadanda suke karkashin ma'aikatar cikin gida.

Yakmut ya ce bayan an kammala gabatar da taron an hada kwamiti cikin gaggawa wacce za ta tabbatar da dokar da aka sanya a hukumomin.

A watan da ya gabata ne hukumar Kwastan ta kasa ta ba da sanarwar daukar ma'aikata dubu uku da dari biyu a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Asali: Legit.ng

Online view pixel