Ku tuba zuwa ga Allah ko mu lalataku da Al-Qunuti – Izala ga masu garkuwa da mutane

Ku tuba zuwa ga Allah ko mu lalataku da Al-Qunuti – Izala ga masu garkuwa da mutane

Kungiyar Jama’atil Izalatil bidi’a wa iqamatissunnah ta gargadi miyagu masu satar mutane babu gaira babu dalili da nufin karbar kudin fansa dasu tuba zuwa ga Allah ko kuma su sha ruwan Al-qunuti daga bakin Malaman kungiyar.

Kungiyar ta bayyana haka ne ta bakin shugabanta, Sheikh Sani Yahaya Jingir yayin taron bude wani katafaren Masallacin Juma’a da aka gina akan dutsen Zainariya dake garin Jos na jahar Filato a ranar Alhamis, 2 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Mutuwa riga: Diyar tsohon gwamnan jahar Neja ta rigamu gidan gaskiya

Ku tuba zuwa ga Allah ko mu lalataku da Al-Qunuti – Izala ga masu garkuwa da mutane

Ku tuba zuwa ga Allah ko mu lalataku da Al-Qunuti – Izala ga masu garkuwa da mutane
Source: UGC

“Musulunci ya haramta satar mutane, hakazalika kundin dokokin Najeriya ya hana garkuwa da mutane, don haka muna kira a garesu dasu tuba zuwa ga Allah, idan kuma ba haka ba zamu fara azumi na musamman da addu’o’I har sai Allah Ya karyasu da ikonsa.” Inji Jingir.

Sheikh Jingir ya bayyana ayyukan masu satar mutane a matsayin zalunci, wanda ya kamata kowa ya hada karfi da karfe wajen yakarsa don ganin an shawo kan lamarin, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sa’annan Shehin Malamin yayi kira ga gwamnatoci a dukkanin mataka da hukumomin tsaro dasu zage damtse wajen kawar da matsalar satar mutane daya yawaita a yanzu ta hanyar samar ma matasa ayyukan yi.

A wani labarin kuma, iyalan Magajin garin Daura, Musa Umar Uba sun bayyana cewa yan bindigan da suka yi awon gaba dashi da daren Laraba sun nemesu a waya, kuma sun bashi dama yayi magana dasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel