Za muyi duk mai yiwuwa Ali Ndume ya janyewa Ahmad Lawan - Kashim Shettima

Za muyi duk mai yiwuwa Ali Ndume ya janyewa Ahmad Lawan - Kashim Shettima

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya bayyana cewa al'ummar Borno za ta samu nasara kan Sanata Ali Ndume domin ya janyewa Sanata Ahmad Lawan, wanda jam'iyyar APC ta zaba matsayin dan takaranta na kujerar shugaban majalisar dattawa.

Shettima ya bayyana cewa a matsayinsu na masu biyayya ga jam'iyya, ya kamata su amince da zabin jam'iyyar kan ahmad Lawan.

Yayinda yake tattaunawa da manema labarai lokacin da kwamitin kamfen Ahmad Lawan suka kai masa ziyara gidansa dake Abuja, Shettima ya ce Sanata Ahmad Lawan ne sanatan APC mafi cancanta da kujeran.

KU KARANTA: Rundunar sojin Najeriya sun samu gagarumin nasara kan yan Boko Haram

"Ba yaki muke da Sanata Ali Ndume ba amma zamu cigaba da yi masa magana ya hada dawo bangaren jam'iyya. Ba yaki muke ba."

"Kana bai kamata inzo nan ba saboda akwai abubuwa uku da nike fama dasu. Ni dan jiha daya ne da Sanata Ali Ndume, kuma na san siyasa ne."

"Na yi imanin cewa jinin da ya hadamu ya fi duk wani abin da muke so. Amma ni mai amincewa ne da zabin jam'iyya, saboda shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara da yardan Allah."

"Mu magoya bayan Sanata Ahmad Lawan ne da Femi Gbajabiamila kuma duk sauran sanatoci da yn majalisan wakilai da jam'iyya ta zaba. Mu mabiya jam'iyya ne da ta baiwa kowa daman takara. ya zama wajibi a girmamata."

Yayinda aka tambayesa shin ya zauna da Ndume kan wannan lamari, Shettima yace "ni ne na gaba a jihar, na nemi shawarin shugabannin Borno kafin yanke shawaran goyon bayan Ahmad Lawan."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel