Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe

Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe

Wata kungiya ta nuna bacin rai akan kiran da majalisar wakilai tayi kwanan nan na cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana a gabanta kan lamarin tsaron kasar.

Maimakon haka kungiyar tace kamata yayi a jinjina wa Shugaban kasar da hukumomin tsaro akan naasarar da suka samu kwanan nan kan yan bindiga da yan akika a jihohin Zamfara da Yobe.

Shugaban kungiyar, Peremobowei Sucess, yayinda yake jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, ya jinjina wa Shugaban kasa Buhari da rundunar soji Najeriya kan sabonta ayyukansu da nasarar da suka samu kan yan ta’addan Boko Haram, yan bindiga da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso yammacin kasar.

Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe
Wata kungiya ta jinjina wa Buhari da hukumomin tsaro kan nasarar da aka samu a Zamfara da Yobe
Asali: Twitter

Peremobowei yace: “Muna sane da cewar bayan tsawaita ziyarar da Shugaban kasar ya kai Dubai, ya gudanar da taro da shugabannin tsaro sannan a karshe ya umurci hukumomin tsaronmu da su hada hannu a ayyukansu sannan su lallasa yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro a kasar.

KU KARANTA KUMA: Ministar kudi ta amince da shawarar IMF kan cire tallafin mai

“Mun kuma yaba da yadda Shugaban kasar ya mayar da martani ga halin da jihohin Zamfara da Kaduna ke ciki. Yadda ya karfafa sannan ya samar da kayayyaki ga sojoji domin magance matsalolin Zamfara da sauran jihohi a arewa maso yamma ya sanyaya zuciyarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel