Shugabancin majalisa: Wata kungiya ta yi tataki zuwa majalisa domin goyon bayan Goje

Shugabancin majalisa: Wata kungiya ta yi tataki zuwa majalisa domin goyon bayan Goje

- Wata kungiya ta bukaci Sanata Danjuma Goje ya fito takarar shugabancin majalisar dattawa

- Shugabanin jam'iyyar APC sun zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin wanda suke so ya yi takarar shugabancin majalisar

- Sai dai duk da haka, Sanata Ali Ndume ya bayyana niyarsa na takarar shugabancin majalisar a ranar Talata 2 ga watan Afrilu

Kungiyar matasan Arewa maso gabas ta goyi bayan Sanata Danjuma Goje mai wakiltan Gombe ta tsakiya a matsayin shugaban majalisar dattawa.

Matasan sun iso harabar majalisar dattawan a ranar Alhamis inda suka bukaci shugabanin jam'iyyar APC su goyi bayan sanata Goje a matsayin shugaban majalisar.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen sojojin Najeriya da ISWA ta hallaka

Shugabancin majalisa: Wata kungiya ta yi tataki zuwa majalisa domin goyon bayan Goje

Shugabancin majalisa: Wata kungiya ta yi tataki zuwa majalisa domin goyon bayan Goje
Source: Depositphotos

'Yan kungiyar sun iso majalisar dauke da takardu masu rubuce-rubuce daban-daban na neman 'yan majalisar su goyi bayan tsohon gwamnan jihar Gombe, Danjuma Goje wanda suka ce zai inganta ayyukan majalisar.

Shugaban kungiyar, Bello Ambo ya ce Sanata Goje ya cancanci ya karbi ragamar mulkin majalisar daga hannun Bukola Saraki.

"Ya samu kwarewa da sanin makaman aiki tun lokacin da ya yi aiki a matsayin Minista da kuma gwamnan jihar Gombe," inji shi.

"A matsayinsa na sanata da ya yi shekaru 8 a majalisa, yana da kwarewar da zai iya tafiyar da ragamar jagorancin majalisar."

Ana sa ran jam'iyyar APC ne za ta fitar da sabon shugaban majalisar dattawa duba da cewa ta dara jam'iyyar PDP da 'yan majalisu 25 a majalisar na dattawa.

Shugabanin jam'iyyar PDP da shugaba Muhammadu Buhari sun goyi bayan Ahmad Lawan na jihar Yobe a matsayin shugaban majalisar.

Sai dai hakan bai hana sauran 'yan majalisan jam'iyyar na APC bayyana sha'awar takarar kujerar shugabancin majalisar ba cikinsu har da Ali Ndume na jihar Borno.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel