'Yan bindiga sun kashe ma'aikacin Lafiya a Gombe

'Yan bindiga sun kashe ma'aikacin Lafiya a Gombe

'Yan bindiga sun kashe wani ma'aikacin lafiya mai sun Mr Audi Gada mai shekaru 43 a karamar hukumar Shongom na jihar Gombe a jiya Laraba 20 ga watan Maris.

Gada ma'aikaci ne da cibiyar kula da lafiya bai daya da ke kauyen Bagunji kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

'Yan bindigan da aka ce adadin su ya kai 13 sun kai farmaki a kauyen ne da safiyar ranar Laraba kuma suka harbe Gada kuma suka yiwa matarsa Lami rauni.

'Yan bindiga sun kashe ma'aikacin Lafiya a Gombe
'Yan bindiga sun kashe ma'aikacin Lafiya a Gombe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Muhawara a kan zaben 2019: Kiris ya rage sanatoci su bawa hammata iska

Dan uwan marigayin, Umar B Alhaji ya shaidawa majiyar Legit.ng a wayar tarho cewa 'yan bindigan sun kai farmaki kauyen ne misalin karfe 12.30 na dare inda suka harbe Gada suka kuma yi tafiyarsu ba tare da sun dauki komi a gidansa ba.

Ya ce a halin yanzu an kai gawar Gada dakin ajiye gawa na babban asibitin garin Billiri.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Mary Malum ta ce ba ta da masaniya a kan afkuwar lamarin a lokacin da aka tuntube ta domin ji ta bakin ta.

A labarin kuma, wani jami'in dan sanda a jihar Legas ya harbe wata yarinya mai suna Hadijat a shagon mahaifiyarta mai sayar da abinci.

Wasu wanda suka shaida afkuwar lamarin sun ce bisa ga dukkan alamu dan sandan yana cikin maye ne a lokacin da ya aikata hakan.

An ruwaito cewa dan sandan da sauran abokan aikinsa sunyi gaggawar tserewa daga wurin bayan sun fahimci yarinyar ta mutu domin gudun abinda fusatattun matasan unguwar za suyi musu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel