Ina da aiki yana jira na ko da an tika ni da kasa a zaben yau – El-Rufai

Ina da aiki yana jira na ko da an tika ni da kasa a zaben yau – El-Rufai

Mun samu labari dazu nan cewa Mallam Nasir El-Rufai ya bayyana abun da zai faru idan ya sha kashi a zaben gwamnonin jihohin da ake yi yau. Gwamnan yana neman tazarce ne a jam’iyyar APC.

Ina da aiki yana jira na ko da an tika ni da kasa a zaben yau – El-Rufai
El-Rufai ya bayyana wadanda za su yi rashi idan ya rasa zabe
Asali: Facebook

Gwamna Nasir El-Rufai yake cewa ko da ace ya fadi zaben gwamna a jihar Kaduna, ba zai rasa aikin yi ba domin kuwa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci zabe. Mal Nasir El-Rufai yake cewa bai sa wannan zaben a kai ba.

Mai girma Gwamnan yana ganin cewa ba zai rasa aikin da zai yi a gwamnatin Buhari ba tun da jam’iyyar APC mai mulki ta lashe zaben shugaban kasa. Gwamnan ya bayyana wannan ne a lokacin da yake kan layin zabe.

KU KARANTA: 2019: Ana shirin zaben sabon Gwamna a Jihar Kaduna

Gwamnan yake fada a cikin raha cewa bai jin wani dar-dar game da zaben da za ayi. Nasir El-Rufai yake cewa ma’aikatan da ke aiki a karkashin sa ne ke tunanin inda za su koma aiki inda APC ta rasa zabe a jihar Kaduna a 2019.

Nasir El-Rufai yayi kira ga jama’a su fito su zabi duk ‘dan takarar da su ke so ba tare da an kawo hatsaniya a zaben ba. Gwamnan mai-ci zai kara ne da Isa Ashiru Muhammad Kudan na PDP.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel