Dan hakin daka raina: Jam’iyyar PRP ta bada mamaki a jahar Bauchi

Dan hakin daka raina: Jam’iyyar PRP ta bada mamaki a jahar Bauchi

Wani abu daya bada mamaki a zaben daya gudana a karshen makon daya gabata shine yadda wata jam’iyyar da ba’a taba tsammani ba, kuma ba’a jin amonta, watau PRP, ta lallasa manyan jam’iyyun nan da suka haskawa, APC da PDP, a jahar Bauchi.

Legit.ng ta ruwaito dan takarar dan majalisa mai wakiltar mazabar Katagum a majalisar wakilan Najeriya a karkashin jam’iyyar PRP, Umar Abdulkadir Sarki ya kai labari, kamar yadda baturen zaben ya tabbatar.

KU KARANTA: Yadda ta kaya tsakanin Atiku da Buhari a jihohi 12 da hukumar INEC ta sanar

Dan hakin daka raina: Jam’iyyar PRP ta bada mamaki a jahar Bauchi
Usman da Malam
Asali: UGC

Idan za’a tuna an taba samun jam’iyyar PRP a jamhuriya ta biyu, kuma jagoranta a wancan lokaci shine marigayi Malam Aminu Kano, wanda ya fafata a siyasar jamhuriyar har ya samu gwamnoni guda biyu, Abubakar Rimi a Kano da Balarabe Musa a Kaduna, tare da yan majalisa da dama.

Sai dai tun bayan wancan jamhuriya, PRP bata sake yin wani tasiri ba, asali ma mutuwa tayi murus, har sai da Alhaji Balarabe Musa ya sake farfado da ita, daga bisani kuma ya mika Alhaji Falalu Bello ragamar tafiyar da jam’iyyar.

Da yake sanar da sakamakon zaben, baturen zaben dan majalisa a yankin, Farfesa Demo Kalla ya bayyana cewa Umar na jam’iyyar PRP ya samu kuri’u dubu ashirin da uku da dari shida da tamanin, 23, 680, wanda hakan ya bashi nasara.

Sauran yan takarar daya kayar sun hada da Ibrahim Muhammad Baba na jam’iyyar APC daya samu kuri’u 18, 976, Maula Adamu na jam’iyyar PDP mai kuri’u 4, 867, da Garba Dogo na jam’iyyar NNPP daya samu kuri’u 8, 983.

A jahar Kaduna ma jam’iyyar PRP tana da dan takara a matakin Sanata, watau Sanata Shehu Sani, wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC, sai dai bai kai labari ba, inda dan takarar jam’iyyar APC, Uba Sani ya lallasa shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel