Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure

Jami'an Rundunar 'Yan Sandan Najeriya sun kama wani magidanci mai shekaru 32, Jibrin Abu da ake zargin ya kashe matarsa, Victoria Aliyu ta hanyar yi mata mummunan bugu da katako saboda yana zarginta da cin amanar aure.

'Yan sanda da ke aiki da caji ofis na Lapai da ke karamar hukumar Lapai na jihar Neja dake a shiyyar Arewa ta tsakiyar Najeriya ne su kayi nasarar kama Magidancin bayan kwarmaton da aka kai masu.

Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure
Wani mai gida ya kashe matarsa saboda zargin cin amanar aure
Asali: UGC

KU KARANTA: An kwace wa matar Jonathan makudan kudade

Legit.ng Hausa ta samu daga majiyar mu ta Northern City wadda ta gano cewar wanda ake zargin ya yiwa matarsa gargadin cewa ta dena amsa wayar abokanta maza amma sai tayi biris da wannan gargadin na sa.

Abu ya yiwa majiyar Legit.ng bayanin abinda ya faru har ta kai ga kisar Victoria a ranar Talata, "Nayi amfani da katoka ne wurin kashe ta bayan na yi mata gargadi sau da yawa a baya domin ta dena amsa wayar gardawa a gidana.

"Ina zargin mata ta tana bin maza a kauyen mu amma a yayin da muke musayar kalamai sai na kashe ta."

Wanda ake zargin ya kuma ce tsohuwar matarsa 'abin kunya ce ga mata saboda ta bata masa suna a gari.

"Tsohuwar mata na tana kawo maza cikin gidan mu na aure kuma al'adar mu ta hana hakan; shi yasa na kashe ta domin in kare suna na da na gidan mu na daga abin kunya," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel