Asalin silar rikici na da Ministan ilmi yana da alaka da rikicin addini – Dr. Bichi

Asalin silar rikici na da Ministan ilmi yana da alaka da rikicin addini – Dr. Bichi

- Tsohon Shugaban TETFund ya bayyana asalin abin da ya sa aka tsige sa

- Abdullahi Bichi yace rikicin sa da Ministan ilmi yana da nasaba da akida

Asalin silar rikici na da Ministan ilmi yana da alaka da rikicin addini – Dr. Bichi

Dr. Bichi banbancin akida ta sa ya bar Hukumar TETFund
Source: Twitter

Tsohon shugaban hukumar nan ta TETfund mai kula da manyan makarantu a Najeriya, Dr. Abdullahi Baffa Bichi yayi cikakken bayani game da tsige sa da aka yi daga aiki a makon nan, inda yace rikicin yana da gami da addini.

A wani bidiyo da ya zo hannun mu, an ji Baffa Bichi yana cewa rigimar da ta shiga tsakanin sa da Mallam Adamu Adamu wanda shi ne Ministan ilmi, ba za ta taba warwaruwa ba saboda a cewar sa, sabani ne irin na addini.

Dr. Baffa Bichi ya fadawa ‘yan jarida cewa akidar babban Ministan ilmin kasar da kuma irin bukatun da ya rika kawo masa a lokacin yana rike da hukumar TETfund sun sabawa dokar kasa. A baya Bichi yayi shigen irin wannan bayani.

KU KARANTA: Fayemi ya bayyana halin da ya tsinci Jihar Ekiti daga PDP

Bichi yace Malam Adamu Adamu yayi kokarin ganin ya tallata wata akidar addini da manufofin ta, wanda a cewar sa idan har yayi hakan, ya ci amanar shugaban kasa da Najeriya baki daya don haka yi tubure har aka yi waje da shi.

Abdullahi Bichi yace na-kusa da Ministan sun dauka za su rika juya sa amma hakan bai yiwu ba. Wannan ne dai ya jawo aka tsige Bichi daga gwamnatin tarayya bayan an ta kai korafin sa gaban shugaban kasa na tsawon lokaci.

Tsohon shugaban na TETfund yayi ikirarin cewa ka’idoji da dokar kasa ya sa a gaba don haka ya ki biyewa irin bukatun da Ministan kasar ya rika bijiro masa da su wanda su ka yi wa dokar kasa karon-tsaye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel