'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa

'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa

'Yan majalisun dokokin biyu a jihar Jigawa sun fice daga jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki sun koma Social Democratic Party (SDP).

Daily Nigerian ta ruwaito cewa kakakin majalisar jihar, Isah Gwaram ne ya sanar da sauya shekan na su a zauren majalisar a yau Juma'a.

A yayin da ya ke karanto wasikarsu, kakakin majalisar ya ce 'yan majalisar da suka fice daga APC sun hada da Muhammad Balangu, mai wakiltan mazabar Balangu da; Usman Masaki-Dansule, mai wakiltan mazabar Kaugama.

Mr Balangu ya ce ya fice daga jam'iyyar APC ne saboda jam'iyyar ta gaza samar da canjin da ta yiwa mutanensa alkawari a shekarar 2015.

'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa

'Yan majalisar dokoki 2 sun fita daga APC a Jigawa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jihohi 10 da suka fi bunkasa a Najeriya a yanzu

Mr Balangu kuma ya zargi jam'iyyar ta APC ta kakabawa 'yan jam'iyyar 'yan takarar da ba su kauna hakan yasa ya yanke shawarar komawa jam'iyyar SDP.

"Nayi rajista da jam'iyyar SDP, ina fatan abubuwa za su canja kuma za a rika sauraron koke-koken al'umma. Ba son rai bane yasa na sauya sheka," inji shi.

Daily Nigerian ta gano cewa ficewarsu daga APC ba zai rasa nasaba da rashin basu tikitin sake takara a jam'iyyar ba a zaben 2019.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa an bawa Mr Balangu tikitin takarar kujerar wakilcin mazabarsa a karkakashin jam'iyyar SDP a babban zabe mai zuwa.

Kazalika, an fahimci cewa an bawa Mr Masaki-Dansule tikitin takarar kujerar sanata na yankin Jigawa ta Arewa-Gabas a jam'iyyar ta SDP.

Mai magana da yawun gwamna Badaru Abubakar, Bello Zaki ya musanta zargin da su kayi na cewa gwamnan ya tilastawa jam'iyyar amincewa da 'yan takarar da ya ke so yayin zaben fidda gwani a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel