Atiku: Buba Galadima ya bayyana a gidan talabijin da rigar APC

Atiku: Buba Galadima ya bayyana a gidan talabijin da rigar APC

Buba Galadima, kakakin kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bawa jama'a mamaki bayan ya bayyana a wani shirin gidan talabijin din Arise TV sanye da rigar jam'iyyar APC domin yiwa Atiku kamfen.

Galadima ya bayyana a gidan talabijin din ne domin kare manufofin jam'iyyar PDP da dan takarar ta na shugaban kasa, Atiku Abubakar.

A kwanakin baya bayan nan ne Galadima ya furta cewar a halin da Najeriya ke ciki a yanzu, tamkar Buhari ya mika mulki ga Atiku ne.

Sai dai ganinsa cikin rigar APC ya bawa jama'a mamaki tare da jawo barkewar cece-kuce a kan manufar sa ta zuwa gidan talabijin domin kare gwaninsa da jam'iyyar sa sanye da rigar jam'iyyar APC mai mulki.

Ko a kwanakin bya sai da Legit.ng ta kwao labarin cewar Buba Galadima, ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da azurta 'yan uwa da dangi.

Atiku: Buba Galadima ya bayyana a gidan talabijin da rigar APC

Buba Galadima a gidan talabijin da rigar APC
Source: Twitter

Da yake magana a wani shirin gidan talabijin na Channels, Galadima ya ce daga cikin 'yan uwan shugaba Buhari da basu da komai kafin 2015, yanzu sun mallaki gidaje a garin Daura, jihar Katsina.

Galadima na wadannan kalamai ne a cikin shirin, yayin mayar da martani ga Sanata Ayo Arise dake kare bangaren gwamnati.

"Shugaba Buhari ya yi alkawarin zai gudanar da sahihin zabe a kasar nan kuma kowa ya yarda da shi saboda mutum ne mai kima. Hakan ne ya sa nima nake cikin masu goyon bayan Buhari," a kalaman Sanata Arise.

DUBA WANNAN: Buhari ya rantsar da muhimman kwamiti 2 karkashin jagorancin Aisha da Dolapo, hotuna

Sai dai Galadima ya ce bai yarda akwai ragowar wata kima a tare da Buhari yana mai bayyana cewar da yawan 'yan uwan Buhari sun zama masu arziki.

"Ni ban ga wata kima da ta rage tattara shugaban kasa ba. Ina kima ga mutumin da ya bar na jikinsa na karbar cin hanci da rashawa. Mun fa san 'yan uwansa, mun san abokansa da talauci ya addaba kafin shekarar 2015.

"Akwai 'yan uwansa da sai mun basu N2,000 kudin mota kafin su iya ziyartar sa a Kaduna, amma yau sun zama biloniyas. Zan iya nuna su ga duk wanda ke son sanin su, a saboda haka babu wata maganar kima tare da shugaban kasa da kuma wannan gwamnati," a kalaman Galadima.

Sannan ya cigaba da cewa, "kaje unguwar masu kudi a Daura ka gani, duk manyan gidajen da zaka ga an gina su kamar a Landan ko Dubai na 'yan uwan Buhari ne. A daina fada min cewar shugaban kasa na da kima ko gwamnatinsa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel