Gwamnatin Ortom ta maidowa da Fillo shanunsa 105 da ta kwace a baya

Gwamnatin Ortom ta maidowa da Fillo shanunsa 105 da ta kwace a baya

- A jihar dai an haramtawa Fulani kiwo

- Anyi ta kashe ni in kashe ka tsakanin makiyaya da mazauna yankin

- Gwamnan jihar ya bar APC ya koma PDP

Gwamnatin Ortom ta maidowa da Fillo shanunsa 105 da ta kwace a baya

Gwamnatin Ortom ta maidowa da Fillo shanunsa 105 da ta kwace a baya
Source: Depositphotos

Tun lokutan da APC ta karbi mulki, aka sami karin kashe-kashe kan kauyuka na manoma a jihohin tsakiyar Najeriya, mai dausayi da albarkar damina, lamari da ake ta'allaqawa makiyaya masu yawon ciyar da shanunsu.

Su dai makiyayan sukan ce an saci shanunsu ne a yankunan da suke kai hari, inda su kuma manoma sukance shanun sun bata musu albarkatun gona, wadanda sunka noma don iyalansu, lamari da ya zamo dan-waken zagaye na kisa da barnar juna.

Ana haka sai gwamnonin yankin musamman Ekiti da Binuwai suka haramta kiwo a gaba daya yankunan nasu, inda a wasu wurare ma ake kwace shhanun da kama makiyayan.

DUBA WANNAN: Abinda Boko Haram ke son cimma kain zaben 2019

Amma a wannan karon, gwamnatin ta sako wa wani jauro da ta kwace wa shanunsa domin kiwo ba bisa ka'ida ba a yankunan Makurdi babban birnin jihar, bayan da ta kama masa shanun har 106.

Kwamishinan noma, Hyacinth Nyakuma ne ya mika shanun a gaban manema labarai, sannan yayi kira ga makiyaya da kungiyoyinsu na Miyetti-Allah Kautal-Horey, dasu kula su bi dokokin jihar na hana kiwo a filin-Allah, domin a sami zaman lafiya.

Ana kira ne ga makiyayan da su nemi wuri su killace dabbobinsu saboda kada su shiga gonakin mutane, su dinga basu abinci in sun nemo sun kwaso, su kuma fulanin sun gwammacewa rayuwar yawo da rangadi don cin ciyayi kyauta, ko ma a wasu lokutan, wasunsu su shiga gonaki da tsakar dare su cinye wa mutane abinci.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel