Uba ya ba yarsa me shekara 3 guba saboda ta fiye kuka a Kano

Uba ya ba yarsa me shekara 3 guba saboda ta fiye kuka a Kano

- Sani Kofar-Gabas, wani mazaunin karamar hukumar Rimin Gado da ke jihar Kano, ya kashe yar’sa mai shekara uku da maganin kashe kwari

- A cewar mahaifin yarinyar ta cika kuka tun bayan da ta samu rauni a kafarta

- Kakakin yan sandan jihar, Magaji Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin

Sani Kofar-Gabas, wani mazaunin karamar hukumar Rimin Gado da ke jihar Kano, ya kashe yar’sa mai shekara uku da maganin kashe kwari.

Da yake tabbatar da lamarin, Magaji Majiya, kakakin yan sandan jihar, ya fada ma manema labarai a raar Litinin cewa Misata Kofar-Gabas ya ba yar’sa maganin kwari wato piya-piya biyo bayan wani karyewa da tayi a kafa.

A cewa Majiya, mai laifin wanda ya amsa laifinsa, yace ya fusata da yar nasa saboda ta fiye kuka ba gaira ba dalili saboda raunin da ta ji a kafar ta.

Uba ya ba yarsa me shekara 3 guba saboda ta fiye kuka a Kano
Uba ya ba yarsa me shekara 3 guba saboda ta fiye kuka a Kano
Asali: UGC

Ya kara da cewa marigayiyar ta fara amai bayan ta sha gubar sannan Kofar-Gabas ya nuna kamar bai san abunda yarinyar ta sha take amai ba sannan ya dauke ta zuwa asibiti inda aka tabbatar da mutuwarta.

KU KARANTA KUMA: Kashe-kashe: Buhari ya ziyarci Zamfara kafin ya fara kamfen a Akwa Ibom – Shehu Sani

Kakakin yan sandan yace bad a jimawa ba za a gurfanar da mai laifin a gaban kotu domin fara shari’a.

Da yake Magana a madadin ahlin gidan, kakan marigayiyar na wajen uwa yace za su tabbatar da cewar an hukunta Saminu Sule akan kashe yar’sa da yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel