Gwamnati za ta kara albashi ba tare da neman cin bashi ba – Shugaba Buhari

Gwamnati za ta kara albashi ba tare da neman cin bashi ba – Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Buhari yace za a karawa Ma’aikatan Najeriya albashi

- Gwamnatin kasar tace za ta ta nada wani kwamiti da zai duba lamarin

- Kwamitin zai yi kokarin gujewa tashin farashin kaya da rashin aikin yi

Gwamnati za ta kara albashi ba tare da neman cin bashi ba – Shugaba Buhari
Gwamnatin Buhari ta sha alwashin karawa Ma’aikata albashi
Asali: UGC

Mun samu labari cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa Gwamnatin sa ba za tayi kasa a gwiwa a game da batun karawa Ma’aikata albashi ba. Shugaban kasar yace ba shakka zai cika wannan alkawari da yayi.

Shugaba Buhari ya bayyanawa ‘Yan Najeriya wannan ne a lokacin da ya gabatar da kasafin kudin shekara mai zuwa a gaban ‘Yan Majalisun Tarayya. Shugaban kasar yace zai kara albashi ba tare da Najeriya ta ci wani sabon bashi ba.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai sa dukiyoyin Barayin Gwamnati a kasuwa

Kamar yadda Shugaban kasar ya bayyanawa ‘Yan Majalisan Najeriya, Gwamnatin Tarayya za ta nada wani kwamiti na musamman domin duba hanyar da za a bi wajen kara albashin Ma’aikatan Najeriya ba tare da aro ko sisin kobo ba.

Shugaban kasar yace idan kwamitin ya kammala aikin sa, zai aikowa Majalisar Tarayya wani kudiri na musamman da zai duba sha’anin karin albashin wajen ganin an dabbaka sabon tsari a kasar ba tare da samun wani sabon cikas ba.

Wannan kwamiti zai dora Gwamnati a kan hanya wajen ganin cewa karin albashin bai zo da hauhuwar farashin kaya ko kuma yayi sanadiyyar da wasu za su rasa aikin yi a kasar ba. Ana sa rai Gwamnati ta karkare aikin a nan gaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel