Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike

Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike

- Ilimi gishirin zaman duniya inji bahaushe

- A Najeriya yankin arewa ne aka bari a baya

- Mata ne koma baya a harkar ilimi

Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike

Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike
Source: Facebook

Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike

Yawan mata daga Arewa wadanda bassu zuwa makaranta a sabon bincike
Source: Depositphotos

Ilimi gishirin zaman duniya inji bahaushe. Amma har yanzu kamar ba hakan bane a arewacin Najeriya. Mata ma sune suka fi karancin ilimin a yankin.

Bincike ya nuna cewa sama da kashi 70.8 na mata masu shekaru 20 zuwa 29 a arewa maso yamma basu iya karatu da rubutu ba Idan aka danganta su da kashi 9.7 na yankin kudu maso gabas na kasar.

Fiye da kashi biyu cikin uku na yammata masu shekaru 15 zuwa 19 basu iya karanta koda jimla daya ba Idan aka danganta su da kashi 10 na yankin kudu.

A jihohi 8 na jihohin arewa, sama da kashi 80 na mata basu iya karatu da rubutu Idan aka danganta su da kashi 54 na mazan jihohin arewa. A jihar jigawa kadai, kashi 94 na mata da kashi 42 na mazan basu iya karatu da rubutu ba.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari yayi wa duniya alkawarin zabuka karbabbu

Kashi 4 a cikin dari na matan arewacin Najeriya ne suka kammala karatun sakandire. Hakan kuwa na shafar ya'yayen da suka ko zasu haifa. Domin kuwa ya'yan mata masu ilimi kashi 50 cikin dari na da yuwuwar rayuwa sama da shekaru 5, sannan kuma akwai yuwuwar su ilimantu.

A fannin kiwon lafiya kuwa, mata 9 cikin 10 masu ilimin gaba da sakandire da kuma kashi biyu bisa uku na mata masu ilimi zuwa sakandire kan haihu a cibiyoyin kiwon lafiya wanda 1 a cikin 10 na mata marasa ilimi ke yin hakan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa.

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel