Kishi ya saka dalibar jami'a ta kashe saurayinta dalibi
Wata dalibar Jami'ar Ladoke Akintola da ke Ogbomoso mai suna Abiodun Olabisi ta kashe saurayinta, Adegun Lekan.
Daily Trust ta ruwaito cewa saurayin da aka kashe ya kammala karatunsa na digiri a jami'ar amma yana jirar takardar zuwa hidimar kasa wato NYSC kwatsam sai wannan tsautsayin ya afku a kansa.
A lokacin da ake gabatar da wanda ake zargi a garin Ibadan a yau Laraba, kwamishin 'yan sanda na jihar Oyo, Abiodun Odude ya ce kishi ne ya yi sanadin rikicin da su kayi har ta kashe saurayin.

Asali: Twitter
DUBA WANNAN: Kisar basarake: An yankewa matar da ta kashe mijinta hukuncin kisa ta hanyar rataya
A cewar Odude, saurayin da budurwarsa suna zaune a gida daya ne kamar yadda wasu daliban jami'a ke yi a gidansu da ke unguwar Phoenix da ke layin Stadium a Ogbomoso a jihar Oyo.
Kazalika, 'yan sandan sun gurfanar da wani lebura, Daniel Segun wanda ake zargi da aikata fashi a dakin kwanan dalibai na jami'ar Lodke Akintola da ke Ogbomoso da kuma wani Aremu Mayowa da ake zargi da aikata fyade ya zamba ta yanar gizo.
Har ila yau, an gurfanar da wasu gungun 'yan fashi da suka hada da Waris Lukman da Sodiq Olabode da suka sace babur a unguwar Olomi da ke jihar da kuma wani dan damfara, Abiodun David da aka samu da laifin damfarar mutane ta yanar gizo.
Odude ya ce rundunar 'yan sandan za ta cigaba da kokarin ta na ganin da kawar da miyagun ayyuka da masu aikata su a jihar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng