Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza

Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza

Shahararriyar jarumar shirya fina finan Hausa, Rahama Sadau, wacce tayi fice da sunan Halwa, tun bayan da ta dauki wani shiri mai taken "Halwa", ta yi bukin murnar zagayowar ranar haihuwarta, cikin salon da ya dauki hankali jama'a, musamman ma maza daga masoyanta.

A ranar 6 ga watan Disamba, jaruma Rahama Sadau, wacce tuni tauraruwarta ta ke haskawa a bangaren shirya fina finan kudancin Nigeria, ta cika shekaru 25 a doron duniya.

Rahama Sadau, ta wallafa wasu zafafan hotunanta a shafukanta na yanar gizo, da suka hada da Twitter da Instagram, ta godewa Allah da ya bata tsawon ran sake ganin wannan rana, tare da gode masa akan dukkanin ni'imomin da ya yi mata.

KARANTA WANNAN: Babachir Lawal ya karyata jawabin Amina Mohammed kan alakanta shi da aikata laifi

Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Asali: Twitter

Jarumar tace: "Na godewa Allah da na samu tsawon kwana har zuwa wata sabuwar shekarar a rayuwata. Godiya ga Allah da na sake ganin wata shekarar cike da dariya, soyayya da kuma ganin abubuwan ban mamaki. Na godewa Allah da wannan kyakkyawar rayuwa mai daraja da ya bani."

Legit.ng Hausa, ta tattara rahoto kan cewa, daga cikin wadanda suka taya jarumar murnar zagayowar ranar haihuwarta, akwai mai tallafawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sadarwa na yanar gizo, Bashir Ahmed, tare da jarumi Ali Nuhu, Adam A Zango, Nuhu Abdullahi, da dai sauran abokanan sana'arta dama furodusoshi kamasu Bashir Maishadda, da kuma daraktoci irinsu Aminu S Bono da dai sauransu.

Kalli Zafafafan hotunan da ta dauka:

Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Asali: Twitter

Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Asali: Twitter

Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Rahama Sadau ta cika shekaru 25: Kalli sabbin zafafan hotunan da suka rikita maza
Asali: Twitter

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

iiq_pixel