PDP: Bamu dauko sojojin haya don gangamin yakin zabe a Sokoto ba, zallar masoya ne

PDP: Bamu dauko sojojin haya don gangamin yakin zabe a Sokoto ba, zallar masoya ne

- PDP ta ce dandazon jama'ar da suka hjjalarci taron gangamin yakin zabenta na nuna goyon baya ga Atiku Abubakar, ba hayarsu ta dauko ba, tsantsar masoya ne

- A cewar PDP, ya zama wajibi ayi watsi da wannan zargi na gwamnan APC na shiyyar Arewa maso Yamma

- Jam'iyyar ta ce taron, wanda ya kafa tarihi a jihar Sokoto, ya hada mambobin jam'iyyar PDP ne kawai da kuma wadanda suka juyawa wa APC baya

Shugaban matasa na jam'yyar PDP, reshen jihar Kaduna Hon. Aliyu Bello ya ce dandazon jama'ar da suka hjjalarci taron gangamin yakin zabenta na nuna goyon baya ga dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, ba hayarsu ta dauko ba, tsantsar masoya ne.

A cewar Aliyu, ya zama wajibi ayi watsi da wannan zargi na gwamnan APC na shiyyar Arewa maso Yamma.

A cikin wata sanarwa wacce shi da kansa ya sanyawa hanu, Aliyu ya ce dandazon jama'ar da suka halarci taron, wanda ya kafa tarihi a jihar Sokoto, ya hada mambobin jam'iyyar PDP ne kawai da kuma wadanda suka juyawa wa APC baya.

KARANTA WANNAN: Buhari ya amince daliban jami'ar NOUN suyi bautar kasa tare da shiga makarantar lauyanci

PDP: Bamu dauko sojojin haya don gangamin yakin zabe a Sokoto ba, zallar masoya ne
PDP: Bamu dauko sojojin haya don gangamin yakin zabe a Sokoto ba, zallar masoya ne
Asali: Depositphotos

Ya ce dandazon jama'ar ya sanya tsoron a zukatan gwamnonin shoyyar Arewa maso Yamma wadanda tuni suka fara hangen faduwarsu a zabe mai zuwa.

"Muna da yakinin samun nasara a 2019 kuma jihar da PDP zata kwace ta a karon farko ita ce Kaduna," a cewar Aliyu cikin sanarwar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Asali: Legit.ng

Online view pixel