Bukola Saraki ya nemi ayi maza a biyawa Ma'aikatan Majalisa bukatun su

Bukola Saraki ya nemi ayi maza a biyawa Ma'aikatan Majalisa bukatun su

Shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, sun umurci kwamitin kula da majalisar dokoki karkashin jagorancin magatakarda, Alhaji Sani Omolori da su magance dukkanin matsalolin da ya sanya ma’aikata zanga-zanga sannan su kawo rahoto kafin Juma’a.

Shugabannin majalisun biyu sun bayar da umurnin ne a wani ganawa da ya samu halartan hukumar kula da majalisar dokoki da mambobin ma’aikata karkashin kungiyar PASAN.

Ku tabbatar kun magance matsalolin ma’aikata kafin Juma’a – Saraki, Dogara ga hukumar majalisar dokoki

Ku tabbatar kun magance matsalolin ma’aikata kafin Juma’a – Saraki, Dogara ga hukumar majalisar dokoki
Source: Facebook

A wata sanarwa daga mai ba Saraki shawara na musamman a kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, shugabannin majalisun biyu sun bayyana cewa yana da matukar muhimmanci karfafawa ma’aikata gwiwa.

KU KARANTA KUMA: Ku taimakawa mijina ya yi tazarce - Aisha Buhari ta roki mata

Saraki da Dogara sun yi umurnin cewa a magance bukatar ma’aikata cikin tsanaki domin a samar da sararin day an majalisa za su iya gudanar da ayyukasu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel